Tulin matsalolin da mu ke fuskata wajen yaki da cutar Coronavirus – Boss Mustapha

0

Sakataren Gwamnatin Tarayya, kuma Shugaban Kwamitin Dakile Cutar Coronavirus, Boss Mustapha, ya bayyana irin matsalolin da ya ce su ke sha musu kai wajen kokarin dakile Coronavirus daga fantsama a kasar nan.

Mustapha ya yi wannan bayani a lokacin da ya ke wa manema labarai bayanin ci gaban da suka samu a cikin watanni uku.

“Ga Matsalolin Yaki Da Cutar Coronavirus” -Mustapha

1. Babbar Matsala ta farko ita ce da har yanzu duk da kokarin da ake yi, har yau ba a samu magani ko makarin cutar Coronavirus ba.

“Kamar yadda sauran kasashen duniya ke ta gaganiyar neman magani ba su samu ba, mu ma a nan har yau mu na ta kokari, amma ba a kai ga dacewa ba.”

2. Akwai kuma mataslar kwrancin wuraren kula da masu fama da cutar da sauran kayayyaki.

3. Akwai matsalar jami’an aiki da sauran ma’aikatan yaki da cutar Coronavirus.

4. Ba a Najeriya kadai ake karancin kayan kariyar jiki daga kamuwa da cutar Coronavirus ba.

Matsalar karancin kayan gwaji da kayan da likitoci da jami’an lafiya ke amfani da su, ta buwayi duniya, saboda sai an kashe makudan kudade kafin su wadaci ko’ina.

To durkushewar tattalin arziki ya sa kasashe raba-kafa. Wato akwai bukatar kudaden gudanar da rayuwa a lokacin da ake bukatar kudaden kariyar cutar Coronavirus.

5. Akwai kuma gagariman matsalolin da a jimlace za mu iya cewa sun kunshi taurin kan jama’a wajen kin yarda da canja takun rayuwa; tsoron yadda ake tsangwamar wanda ya kamu da cutar Coronavirus; tababa da shakku ko kin gaskata cutar; tasirin al’ada, addini da sauran tunanin da masu bijire wa ka’idonin kiyayewa daga cutar Coronavirus ke fakewa da su.

“Coronavirus, Kogi Cinye Mai Gardama” – Kodinatan Korona

Da ya ke ci gaba da bayani, Kodinetsn Yaki da Coronavirus na Kasa, Sani Aliyu, ya ce a yanzu ne ma jama’a da dama za su fi shiga tarkon saurin kamuwa da Coronavirus fiye da can baya.

Ya a yanzu cutar ke ci gaba da kara fantsama a cikin al’umma lunguna da sakuna.

“Gaskiyar magana ita ce ba za mu lamunta da irin yadda jama’a ke bijire wa dokoki da ka’idojin kiyayewa da cutar Coronavirus ba.”

“Ba Mu San Ranar Da Najeriya Za Ta Kakkabe Coronavirus Ba” -Sani Aliyu

Kodinetan Yaki da Coronavirus na Kasa, Sani Aliyu ya ce: “Kamar yadda na taba fada kwsnakin baya, a gaskiya babu lokacin da za mu iya yin kintace ko kirdadon sa’adda za a iya rabuwa da cutar Coronavirus a kasar nan ba. Saboda a yanzu ne ma cutar ke ta kara kutsawa cikin al’umma bagatatan. Kuma sai kara fantsama ta ke yi a jihohi daban-daban.

“Yanzu Aka Fi Kamuwa Da Cutar Da An Shiga Jama’a”

“Yanzu da mutum ya shiga cikin gungun mutane, da wuyar gaske bai koma gida dauke da cutar ba, idan bai yi taka-tsantsan ba. Saboda a yanzu ake kasa samu dimbin masu kamuwa da cutar kamar barkewar wutar-daji.”

Share.

game da Author