Jihar Kano ta wayi garin Alhamis da labarin rasuwar Farfesa Mansuru Lasu-Eniola, na Jami’ar Bayero a Kano.
Farfesan ya rasu ne a ranar Laraba a Asibitin Duba Marasa Lafiya na cikin jami’ar.
Kafin razuwar sa shi ne Shugaban Fannin P.H.E na jami’ar, kuma dan asalin Jihar Oyo ne.
Da ya ke sanarwar rasuwar Farfesa, wani babban malami a jami’ar, Garba Sheka, ya ce Mansuru ya rasu bayan wata takaitacciyar rashin lafiya.
Ba a dai bayyana rashin lafiyar da ta yi sanadiyyar mutuwar farfesan ba.
Yayin da ake fama da yawaitar mace-mace a birnin Kano, Mansuru shi ne farfesa na bakwai da suka mutu a Kano cikin kwanaki 12.
Farfesa Aliyu Dikko ne ya fara mutuwa a ranar 25 Ga Afrilu, sai Farfesa Ibrahim Ayagi, wanda tsohon mashawarcin tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ne, na fannin Tattalin Arziki.
Farfesa Balarabe Maikaba na Jami’ar Bayero ya rasu a ranar 26 Ga Afrilu, sai kuma shi da Farfesa Sabo Kurawa duk a rana daya.
Ranar 27 Ga Afrilu kuma an tashi da rasuwar Uba Adamu, mahaifin Shugaban Jami’ar da ake karatu daga gida, NOUN.
Kano ta yi rashin Farfesa Isa Hashim, wanda kafin rasuwar sa shi ne Jarman Kano.
A ranar 27 Ga Afrilu har wa yau dai Farfesa Ghali Umar na Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Kano ya rasu.
Tun da aka fara wannan yawan mace-mace, a kullum abin ba raguwa ya ke ba. Wakilin mu ya tabbatar da cewa Jihohin Barno, Jigawa, Sokoto da Katsina ma duk ana fama da wannan yawaitar mace-mace.