Kwamishinan kiwon Lafiya na jihar Jigawa, Abba Zakari, ya bayyana cewa cikin Almajiran da aka dawo da su daga Kano zuwa jihar 16 sun jijjibo Coronavirus daga can Kanon.
Kwamishina Abba yace, an dibi samfarin almajirai sama da 600 amma na mutum 45 ne aka dawo da su. 16 cikin su kuma na dauke da cutar.
Zakari yace wadanda basu kamu ba za a maida su ga iyayen su kuma za a raka su da tukuicin naira 10,000 kowannen su da kayan sawa.
Su kuma wadanda ke dauke da cutar za akillace su a ci gaba da basu magani har sai sun warke daga cutar.
An maido wa jihar jigawa Almajirai 1,114 daga jihohin Kano, Kaduna, Gombe da Nasarawa.
Idan ba a manta ba, Gwamnatin Jigawa ta nuna matukar damuwa da fargabar yadda ake yawan samu masu dauke da cutar Coronavirus a jihar.
A ranar Talata ta ce fantsamar cutar a cikin al’umma na kawo barazana sosai ga rayuwar dimbin jama’a.
Sannan kuma gwamnatin ta nuna fargaba dangane da yadda ake yawan mace-mace a jihar, mutuwar da har yau an kasa gane dalili ko musabbabi.
“Sabbin adadin alkaluma 32 da aka samu a jihar Jigawa, ba daga almajirai aka same su ba. Duk an same su ne daga cikin jama’a. Saboda haka matsawar jama’a ba MU ciki gaba da addu’o’i da zaman gida da kuma kiyayewa da sauran ka’idojin kauce wa kamuwa da cutar ba, to za ta ci gaba da yaduwa a cikin jama’a.”
Haka wani hadimin Gwamna Badaru Abubakar, mai suna Zakari Kafin Hausa ya shaida wa PREMIUM TIMES.
“Yawancin wadanda ake samu da cutar nan, idan aka debi samfarin jikin su aka kai awo, akan gargade su cewa su zauna wuri daya su killace kan su.
“Sannan da yawan mutane ba su ma yarda akwai ta ba. To ka ga irin haka ke haddasa karin yaduwar cutar da fantsamar ta cikin jama’a.”