Hukumar Kula da Ma’aikatar Kula da Harkokin Man Fetur (NNPC), ta bada sanarwar cewa ta rage kashi 17.94 na farashin kowace litar man fetur a farashin da dillalan fetur da sauran masu gidajen mai ke sayen sa kai-tsaye daga daffo.
A watan da ya wuce dai aka rage farashin sa daga daffo, daga naira 113.32 kuwa naira 108 kowace lita.
A yanzu kuma ana sauraren NNPC za ta bayyana sabon farashin man, wanda zai kasance an samu ragin kashi sama da 17% na farashin sa a yanzu.
Sabon farashin zai zo ne sakamakon wani alkawari da Shugaban NNPC, Mele Kyari ya yi cewa a farkon kowane wata, za a bayyana sauyin farashin litar man fetur a kasar nan.
Wannan sassauta farashin litar danyen mai ga ‘yan kasuwa masu saye kai-tsaye daga daffo, zai sa a rage farashin litar mai a gidajen mai kenan a fadin kasar nan.
Hukumar Kayyade Farashin Litar Man Fetur (PPPRA) ce za ta bayyana sabon farashin na wannan wata da mu ke ciki.
A wancan tsohon farashi da ake sayar wa dillalai lita daya a kan naira 113.28, an amince su sayar a gidajen mai a kan naira 125 a gidaje masu nisan-zango. Su kuma gidajen mai masu gajeren-zango, su na sayarwa a kan naira 123.5.
Kakakin Yada Labarai na NNPC, Kenneth Obateru, ya ce Shugaban Hukumar Kula da Hada-hadar Sayar da Man Fetur na Kasa, Musa Lawan ya ce an bijiro da wannan sabon farashi ne domin a kara samar da kasuwa ga man fetur sosai, yadda za rika sayen sa da yawa.
Hukumar Kula da Cinikayyar Man Fetur, PPMC ta ce ana neman kasuwar man fetur ne saboda bilyoyin litar man fetur na nan jibge a kasa ya yi cumbu.
Rahotanni daga wasu jaridu sun tabbatar da cewa yanzu haka akwai gangar danyen mai bilyan 82 na Najeriya da ke damkare cikin jiragen ruwa a bakin teku, wadanda ake neman masu saye a duniya, amma an rasa.
Discussion about this post