Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan, ya bayyana aniyar cewa zai janye jiki daga siyasa domin ya kama aiki gadan-gadan na agaji, jinkai da taimakon al’umma.
Jonathan ya yi wannan kalami ne wurin kaddamar da Shugabannin Kwamirin Zartaswa na jam’iyyar PDP a Jihar Bayelsa, a Yenagoa, babban birnin jihar.
Ya ce ya na so ne ya maida hankali ka’in-da-na’in wajen karfafa Gidauniyar Tallafin Jonathan, domin a cewar sa, hakan zai ba shi damar sake yi wa al’ummar kasar nan ayyukan alheri sosai.
Kada Guyawun Ku Su Yi Sanyi: “Ina jan hankalin ku cewa kada zuciyoyin ku su karaya, kuma kada guyawun ku su yi sanyi, idan nan gaba ku ka daina gani na a tarukan siyasa. Ko wannan ma na zo dai ne kawai gudun kada ba a gan ni ba, a rika surutan neman sanin dalili.
” Mutanen da zan hada karfi da su wajen aikin wannan gagarimar gidauniya tawa, su na ganin cewa idan ina tsoma kada a siyasa, to ba za a rika runguma ta hannu bi-biyu ba, za a rika nesa-nesa da ni. Shi ya sa na yanke shawarar janye jiki na daga siyasa.
“Ni ina ganin tunda har na kai ga rike matakin shugaban kasa, to zai fi kyau na saki layin siyasa haka nan, na kama wani layin wanda zan amfana wa al’ummar kasar nan baki daya da jihar nan.” Inji Jonathan.
A karshe ya gode wa Gwamnan Jihar Bayelsa Douye bisa kokarin da ya ke yi wajen ciyar da jihar gaba.
A nasa bangaren, gwamna Douye ya yi kira ga ‘yan PDP su kara hada kan su, kuma ya yi gargadin cewa kada a yi siyasa da gaba, kuma kada a yi bi-ta-da-kulli.
Cikin wadanda suka halarci taron, har da tsohon gwamna Dickson da Shugaban Jam’iyyar PDP na Kasa, Uche Secondus.
Discussion about this post