Wasu bayanan shafuka 50 da Gwamnatin Ingila ta buga a ranar Litinin, sun nuna cewa za a koma ci gaba da gasar Premier League a ranar 1 Ga Yuni, 2020.
Bayanan ga gwamnati ta buga sun nuna matakan da za a rika bi daya bayan daya wajen ci gaba da sake bude harkokin rayuwa da mu’amala a Ingila, tun bayan da annobar Coronavirus ta dagula duniya baki daya, har aka dakatar da komai, ciki har da wasannin kwallon kafa a duniya.
Mataki na biyu da Gwamnatin Boris Johnson ta gindaya, shi ne sake bude filayen kwallo domin a karasa gasar Premier League a kasar, amma ba tare da ‘yan kallo ko da mutum daya ba.
Sai dai kuma ana sa ran a cikin watan Yuli za a iya barin ‘yan kallo shiga kallon wasannin, saboda a tsare-tsaren bude harkoki a mataki na uku, za a sake bude gidajen sinimomi da gidajen aski da wankin gashi da kitso da sauran makamantan su.
“Amma kuma ba za a yi saurin bude wararen duk da aka san cinkoson mutane zai yi wahalar a bi doka da ka’idar kauce wa daukar cuta ba.”
“Gwamnati za ta ci gaba da duba irin ci gaba da nasarorin da ake samu a wasu kasashen da suka rigaya suka bude wasu wuraren gudanar da harkoki.
“Kuma gwamnati za ta kafa kwamitin bibiya da sa-ido da dubagaein yadda al’amurra ke gudana. Wannan kwamiti zai yi aiki kafada-da-kafada da dukkan bangaeorin da ke da ruwa da tsaki a wuraren kasuwanci da hada-hadar aka bude.”
Wannan bayani na gwamnati ya yi nuni da cewa ko da an kyale masu kallo su shiga filayen wasa nan gaba, to ba dafifi za a fara yi ba tukunna. Za a rika shiga ba da yawa ba, gwargwadon yadda aka ga cutar Coronavirus na raguwa, to sai a rika barin ‘yan kallo na kara yawa a sitadiyan kenan.
Ana ganin cewa karasa wasan zai ba Liverpool FC damar lashe kofin a ruwan sanyi, domin ta rigaya ta cinye ruwon, saura ta side kwano kawai, don kada kudaje su dame ta.