CORONAVIRUS: Masu Otal-Otal a Abuja na ta rusa kukan rashin kwastomomi

0

Wasu masu otal-atal a Abuja, babban birnin Tarayyar Najeriya, sun koka dangane da yadda kasuwar su ta durkushe sakamakon gugurguza tattalin arziki da annobar Coronavirus ta yi.

Baya ga kamfaninin sufurin jiragen sama, masu otal-otal na a sahun gaban wadanda matsin tattalin arziki ya rugurguza a kasar nan.

Kulle jihohin Lagos, Ogun da Abuja da sauran garuruwa da aka yi, ya haifar da tsayawar harkokin kasuwanci da sauran hada-hada cak.

Haka nan kuma tsaida zirga-zirgar jiragen sama a duniya da cikin kasa, ya sa baki sun daina shiga Abuja. Wadanda kuma ke cikin birnin, suka rika kokarin ficewa domin komawa garuruwan su.

Dalilin haka, an gudu an bar Abuja tamkar kango, saboda haka zirga-zirga da kuma tsoron kamuwa da cutar Coronavirus, kasancewa shi ne birnin na biyu da cutar Coronavirus ta fara bulla, banda Lagos.

Asara Goma Da Ashirin: Manyan otal irin su Hilton, sun kasance babu kowa, babu bargar motocin alfarma na manyan bakin da ake ajiyewa a wuraren ajiye motoci.

A wurin karbar baki ma babu kowa. Mabu karakainar ma’aikatan otal da jami’an tsaro.

Kayayyakin abinci da na lashe-lashen da aka saba dabdalar ci da sha, duk sum lalace an zubar da su.

‘Mutum Milyan 8 Sun Rasa Aiki A Fannin Zirga-zirga: Masana sun danganta rugukewar harkar otal da rasa aikin da kusan mutum milyan 8 suka yi a fannin sufuri da yawon bude ido. Saboda wadannan bangarorin ne suka fi kashe kudade a Otal-Otal.

Masu ruwa da tsaki a bangaren sun nemi a gaggauta kai daukin kudade a bangaren, musamman a Afrika, domin idan ba a yi hakan ba, to harkar za ta durkushe milyoyi su rasa aikin dogaro da kan su.

Ota-Otal A Hotel

Duk da cewa Kakakin Yada Labarai na Hilton Hotel, Ijeoma Osuji ta ki yarda ta zanta da wakilin mu, amma dai wasu jami’an tsaron otal din sun ce babu wani ma’aikaci ko.daya a ciki.

“Tun a makon karshe na watan Mayu aka daina aiki a otal din Hilton. Babu kowa babu bako ko daya a ciki. ‘yan ma’aikatan da muka rage mu na wurin ne saboda kantinan da ke kasa wajen sayar da jaridu akwai kayyaki a wuraren.”

Amma dai bai ce an tsaida musu alnashi ko kuma ana biyan su ba.

Babban Jami’in Newland Luxury Hotel, Uche Osongi, ya ce duk da sun rufe ba a aiki kuma ba a samun kwastomomi, kuma ma’aikata duk su na gida, hakan bai haka otal din ci gaba da tafka asara ba.

“Mu na ci gaba da kashe makudan kudade wajen biyan kudin watar lantarkin da mu ke kunnawa da ruwa da sauran su.

“Batun albashi kuwa, a gaskiya sai dai idan an dawo aiki mu samu mu rika biyan ma’aikatan ariyas na watannin da ba mu biya ba.

“Batun kwastomomi kuwa, ai tuni babu ko daya tal a ciki. Wa ke kwastoma, tunda an ce kowane ma’aikacin otal ya yi zaman sa a gida!”

Kakakin Yada Labarai ta Kungiyar Masu Otal-Otal, Fummi Kazeem ta ce idan ba a gaggauta ceto ma’aikatan Otal-Otal ba, to ba da jimawa ba za su afka mummunar rayuwar da za ta iya kai wasu aika munanan ayyukan assha.

Share.

game da Author