Hukumar Kula da Gidajen Kurkuku Kasa na ci gaba da kantara wa Gwamnatin Tarayya karya da yi mata rufa-rufar hakikanin gaskiyar abin da ya faru dangane da bude wuta da kisan daurarru a Kurkukun Kaduna.
Bayan hukumar ta shimfida wasu karairayin a makon da ya gabata, daga baya kuma ta fadi gaskiya, bayan PREMIUM TIMES ta fallasa hakikanin gaskiyar abin da ya faru, a wannan makon kuma ta sake kantara wasu karairayin, inda ta nuna cewa dukkan wadanda suka mutu a tarzomar duk wadanda aka rigaya aka yanke wa hukuncin kisa ne, ba wadanda ke jiran a yanke musu hukuncin kisa ba ne.
Tun a ranar da al’amarin ya faru hukumar ta fata nunke gwamnatin tarayya baibai, ta ce ba a kashe kowa ba.
Amma da PREMIUM TIMES ta fallasa sunayen wadanda aka kashe, sai Shugaban Kurkukun Kaduna, Sanusi Danmusa ya fitar da sanarwar ta ya kara kantara wata karyar, ya ce wadanda aka kasje din duk wadanda aka rigaya aka yanke wa hukuncin kisa ne.
An Kure Ramin Karya: Babu Wanda Aka Yanke Wa Hukuncin Kisa A Cikin Su
PREMIUM TIMES ta sake fallasa wadannan sabbin karairayi, inda ta binciko kuma ta zakulo sunaye da bayannan shari’un wadanda aka bindige a yayin tarzomar. Kuma ta gano ba wadanda ke jiran a aiwatar da kasa a kan su na ne, wadanda ke kan shari’a ne.
Ga bayanai da sunayen su dalla-dalla.
1. Hammed Abdullahi mai shekaru 25 da aka bindige har yau ba aka kai ga yanke masa hukunci a Babbar Kotun Kaduna Lamba 5 ba. Ana tuhumar sa da laifin kisa, amma ba a kai ga tabbatar da zargin ba.
2. Lucky Ujokama, dan shekara 24 da aka kashe shi ma ya na fuskantar shari’ar zargin fyade a Kotun Majistare ta 17 da ke Barnawa, Kaduna.
3. Yahu Salisu shi ma ba a kai ga yanke masa hukunci a shari’ar da ake tuhumar sa a Kotun Majistare ta 21 ba, da ke kan titin Ibrahim Taiwo, Kaduna.
4. Ibrahim Abubakar mai shekaru 37, an bindige shi, kuma ba a kammala shari’ar da ake tuhumar sa sa laifin fashi da makami ba, ballantana a yanke masa hukuncin kisa.
Sauran Wadanda Aka Jikkata
Akwai Oguma Osaronu da kuma Oluchukwu Oxhe da aka jikkata, har yau su na cikin mawuyacin hali a asibiti.
Sai kuma Wisdom Felix, ya ci dukan tsiya har aka sumar da shi. Tun makon jiya, kuma majiyar PREMIUM TIMES ta ce har yau bai farfado ba. Bai san inda ya ke ba.Har yanzu Felix na fuskantar shari’a ne a Babbar Kotun Kaduna ta 3.
Samuel Sunday an dirka masa harbi, da ya ke akwai kwana a gaba, bai mutu ba, amma a halin yanzu ya na bukatar a yi masa tiyata.
PREMIUM TIMES ta samu bayanan shari’un su da ke a kotu. Hakan kuwa ya kara tabbatar da cewa dukkan su na a yanke musu hukuncin kisa, kamar yadda Sanusi Danmusa ya bayyana ba.
Cikin makon da ya gabata PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda jami’an tsaro suka bindige ‘yan bursuna biyar a kurkukun Kaduna, cewa sabanin yadda daga farko Jami’an Hukumar Gidajen Kurkuku suka kantara karya cewa babu wanda aka kashe a wurin tarzomar, PREMIUM TIMES ta tabbatar da cewa jami’an tsaro sun kashe daurarru har biyar a tarzomar, wadda ta tashi cikin kurkukun Kaduna.
Sannan kuma PREMIUM TIMES ta tabbatar da cewa an yi wa Jami’an tsaro 16 rauni. Har yanzu kuma goma daga cikin su na kwance a wani asibiti da ba a bayyana sunan sa da inda ya ke a Kaduna ba. Amma an rigaya an sallami sauran shida din.
Tun a ranar Talata ce dai wasu daurarru a gidan kurkurun suka tayar da tarzoma, bisa zargin cewa wata mata da ke tsare ta kamu da cutar Coronavirus, har ma an garzaya da ita asibiti.
Kafin sannan kuma akwai tuburrewar umarnin da Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola ya bayar, cewa a rage cunkoson gidajen Kurkuku a kasar nan. Aregbesola dai ya samu wannan umarni ne daga shawarar daga Kwamitin Shugaban Kasa mai Yaki da Coronavirus.
Yadda Tarzomar Ta Barke
Al’amarin ya faru bayan an kawo wata mata an tsare. Ba a dade ba sai ta fara rashin lafiyar da ke da alamun kamuwa da cutar Coronavirus.
Majiya a cikin kurkukun ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa daga baya sai labari ya cika gidan kurkukun cewa matar ta mutu a asibiti.
To dama kuma yawancin daurarrun duk su na cikin zaman jiran za a sallame su ne, saboda Kwamitin Shugaban Kasa ya ce a sallami wasu daurarru da dama, domin a rage cunkoson da ka iya haifar da Coronavirus.
Me zai faru, maimakon daurarru su ji an fara kiran sunayen su ana sallamar su, sai ma suka fahimci an hana duk masu kai musu ziyara ko kai musu abinci daga gida shiga cikin kurkukun.
“Ganin haka sai hatsaniya ta kaure, har daurarrun suka fara yi wa Jami’an kurkukun sababi. To gayyato jami’an tsaro dauke da bindigogi daga waje, ya munanta tarzomar, domin bude wuta kawai suka yi.
PREMIUM TIMES ta tabbatar cewa wani wanda ake tuhuma da laifin kisa ne mai suna Hammed Abdullahi ne aka bindigewa. Sai kuma wani Lucky Ugokam da ake tuhuma da laifin fyade.
An kuma harbi wani mai suna Yahu Salisu a duwaiwai, daga bisani ya rasu.
Sauran mutane biyu kuwa, Ibrahim Abubakar da ake kira Lolo, shi da wani da aka yanke wa hukuncin kisa kisa mai suna Olochukwu Iche, an rika zabga musu azaba ce har ran su ya fita.
Rufa-rufar Jami’an Tsaro
Binciken PREMIUM TIMES ta karkashin kasa a kurkukun ya tabbatar da cewa jami’an tsaro sun gigice wajen kokarin yin rufa-rufa, domin kada a kama su da laifin kisan daurarrun.
Majiya ta shaida wa jaridar nan cewa an yi kokarin shafa wa wasu daurarru kashin kaji, aka ce su rubuta bayani a rubuce cewa su ke da laifi.
“Amma wani da ya ki amincewa, cewa ya yi sai dai a kashe shi, amma shi ba zai dauki laifi da bai yi ba, ya ce ya yi.”
Wata majiya kuma ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa lokacin da aka yi tarzomar ba a karya makullan kofa ko daya ba.
“Amma washegari sai mu ka ga jami’an kurkukun sun balle wasu makullai da kofofi, domin su kafa shaidar-zir cewa wai kokarin tserewa daurarrun suka yi, har suka balle kofofin dakunan su.”
Sanann kuma majiyar ta kara da cewa, “mun ga an kawo wasu da dare lafiyar su kalau. Amma washegari sai mu ka ga kowanen su da bandeji. Su za a nuna a ce jami’an tsaro ne da aka ji wa rauni.
Da PREMIUM TIMES ta kira kakakin gidan kurkukun kasar nan, Austin Njoku, sai ya karyata cewa an yi kisa. Ya ce ko harbi ma ba a yi ba, kuma ya na kan hanyar zuwa Kaduna domin ganewa da idon sa.
Daga baya ranar Juma’a da aka bayyana masa hujjojin cewa an kisa, sai ya nuna cewa ya na jiran ogan su kwata-kwata ya fitar da bayani tukunna.
Daga baya ya tabbatar da bayanan PREMIUM TIMES tare da cewa an ji wa jami’ai 16 rauni.
Tuni dai kungiyoyin kare hakkin dan Adam suka shiga rikicin tsamo-tsamo, domin kare hakkin daurarru. Sun kuma yi tir da abin da jami’an tsaron suka yi musu.
Discussion about this post