Shugabannin Majalisar Dattawa da Tarayya ba su yarda da tsarin rabon kudaden agajin Coronavirus ba

0

Shugaban Majalsar Dattawa da na Majalsar Tarayya, sun nuna rashin gamsuwa da rashin amincewa da tsarin da Ministar Ayyukan Agaji, Jinkai da Inganta Rayuwar Jama’a ta bi wajen rabon makudan kudaden da ta ce ta rabas ga talakawa domin rage musu radadin kuncin zaman gida a lokacin zaman kauce wa kamuwa da cutar Coronavirus.

Sanata Ahmed Lawan na Majalisar Dattawa, ya nuna rashin amincewar sa a gaban Minista Sadiya Farouq, lokacin da suka gayyace ta domin ta yi musu karin haske daga kura-kuran da jama’a da dama a kasar nan ke zargin an tabka nara rashin adalci a lokacin raba kudaden.

Lawan ya yi kira a gaggauta kafa dokar da za yi daidai da tsarin rabon kaya da kudaden tallafi na sauran kasashen duniya da duniyar ta amince da shi.

Lawan ya fito karara ya shaida wa minista cewa ba a yi adalci a wajen rabon ba, domin a cewar sa, ba wadanda suka cancanta ko suka wajaba aka bai wa kudaden ba.

“Domin idan an ce ta intanet za a tantance talaka ko aka tantance talaka, to kenan ba talaka na hakika aka raba wa kudin ba.

“Tantirin talaka fa ba shi da sukunin intanet ko banki ajiyar kudi, ba shi da lantarki kuma ba shi ma da lambar makullin asusun banki, wato BVN.

Daga nan Lawan da Femi Gbajabiamila sun nemi sadiya ta sauya tsarin bayar da kudaden gaba daya.

Ana ci gaba da sukar Sadiya dangane da yadda ta ce ta raba naira bilyan biyar ga talakawa a cikin kwanaki biyu.

Wasu na ganin ko naira bilyan biyu ba a ma raba.

Shi ma Sanata Lawan ya tambayi tssrin da aka bi aka raba kudaden da kuma yankuna ko jihohin da aka raba kudaden, kai da ma sauran tamayoyi masu dora shakku a kan Minista Sadiya.

Idan ba a manta ba, ta sha ragargaza a shekarar da ta raba dabinon tallafi daga Saudiyya a lokacin azumi, sa’adda ta ke shugabancin Hukumar Raba Kayan Agaji.

Share.

game da Author