Sanarwar hukumar hana Yaduwar Cututtuka ta Kasa NCDC ranar Talata ya nuna cewa an samu karin mutum 16-da suka kamu da coronavirus a Najeriya.
Sakamakon gwajin da NCDC ta yi ya nuna cewa an samu karin mutum 16 daga jihohi 3 da Abuja a kasar nan.
10 a jihar Legas, 2 a Abuja, 2 a Oyo, 1 a Delta sannan 1 a Katsina.
Hukumar ta ce 44 sun warke sannan shida sun mutu.
Legas -130
FCT – 50
Osun – 20
Oyo – 11
Akwa Ibom – 5
Ogun – 4
Edo – 11
Kaduna – 5
Bauchi – 6
Enugu – 2
Ekiti- 2
Ribas – 1
Benuwe – 1
Ondo – 1
Kwara – 2
Delta – 1
Katsina – 1
Jihar Katsina ce jiha ta biyu a yankin Arewa Maso Yamma da aka samu da mutanen da suka kamu da cutar. Jihar Kaduna na da mutum 5 zuwa yanzu.
Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta yi suka da kakkausar murya cewa babu wani masanin kimiyya ko likita da zai gwada maganin coronavirus a Afrika
Kungiyar ta ce irin wannan kalamai da likitocin Faransa suka yi ya saba wa dokokin hukumar kuma ba za ta amince da shi ba.
WHO ta ce hukumar zata bi ka’idar yadda ake yin gwajin magunguna idan aka yi su ba tare da an zabi can ko kuma ayi a wani yanki don nuna wani bambanci ko fifiko ba.