Gwamnatin tarayya ta umarci ma’aikatan gwamnati tarayya daga mataki na 12 zuwa sama su koma aiki daga ranar 4 ga watan Mayu.
Gwamnati ta ce daga wannan rana ma’aikata za su rika zuwa aiki sau uku a mako wato ranar Litini, Laraba da Juma’a sannan su tashi aiki karfe 2 na rana.
Shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya (HOCSF) Folasade Yemi–Esan ta Sanar da haka ranar Alhamis a wani takarda wanda darektan yada labaran hukumar Olawunmi Ogunmosunle ya saka wa hannu,
Yemi-Esan ta ce yin haka na daga cikin matakan sassauta dokar zaman gida dole da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya saka domin hana yaduwar cutar coronavirus.
Bisa ga wannan sanarwa ma’aikata za su koma aiki tare da kiyaye sharuddan kamuwa da yada cutar.
Sai ya zama dole za a bari wani ya ziyarci ma’aikaci a ofis, sannan idan har za a zo sai bako ya saka takunkumin fuska.
Za kuma a saka ruwa da sabulu a ko ina a ofisoshin gwamnati da hukumomi domin ma’aikata da baki su rika wanke hannayen su idan suka ziyarci ofisoshin.
Za kuma a rika amfani da na’uran gwada zafin jiki ga duk wanda zai shiga ma’aikata ko hukuma.
Gwamnati ta yi wa duk ofisoshin dake ma’aikatu da hukumomi feshi domin kashe kwayoyin cutar coronavirus.
Idan ba a manta ba a ranar 27 ga watan Afrilu ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sassauta dokar hana walwala a jihohin Legas da Ogun da Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Daga ranar 4 ga watan Mayu, za a ci gaba da walwala tun daga karfe 9 na safe zuwa karfe 8 na dare, daga nan kuma za a shiga kulle sai safiyar gobe.
Hakan na nuni cewa shugaban kasa ya kara wa jihohin har da Abuja ‘Zaman Gida Dole’ na mako guda kenan.