Mataimakin gwamnan jihar Yobe kuma shugaban kwamitin dakile yaduwar cutar Covid-19 Idi Gubana ya ce mutum daya ya kamu da cutar a jihar.
Ya ce a bincike ya nuna mutumin bashi ta tarihin yin tafiye-tafiye zuwa jihohin da cutar ta bullo sannan bai yi cudanya da wani da ya kamu da cutar ba.
Gubana ya fadi haka ne wa manema labarai a garin Damaturu ranar Laraba.
Ya ce mutumin na da shekaru 29 a duniya kuma yana zaune da iyayensa a garin Damaturu.
A ranar 23 ga watan Afrilu wannan matashi ya kai Kansa asibitin Damaturu inda ya bayyana wa likita yadda yake fama da zazzabi, ciwon makogoro da tari.
Nan da nan aka yi masa gwajin cutar inda sakamakon ya nuna cewa ya kamu da cutar.
Gubana ya ce ma’aikatar kiwon lafiya sun fara neman mutanen da suka yi cudanya dashi domin killace su da yi musu gwajin cutar.
Ya kuma yi kira ga mutane da su kwantar da hankalinsu kuma kiyaye sharudan gujewa kamuwa da cutar da ma’aikatan kiwon lafiya suka bada.
Idan ba a manta ba a ranar Laraba ne jihar Yobe ta shiga sawun jihohin da cutar Covid-19 ta bullo a Najeriya.
Hakan ya kawo adadin yawan mutanen dake dauke sa cutar zuwa 1728.
An sallami 308 sannan 51 sun mutu a Najeriya.