Rincabewar da cutar Coronavirus ta yi a Kano na ci gaba da kara tayar da hankulan jama’a a ciki da wajen jihar, duk kuwa da isar da Tawagar Shugaban Kasa Mai Dakile Coronavirus ta yi a Kano, a karkashin dan asalin jihar Dakta Nasiru Gwarzo.
Akwai batutuwa da dama masu wahalar warwarewa a Kano, wadanda duk wani kokari da za a iya yi domin dakile cutar, su ne ka iya kawo cikas, ba kamar Abuja da Legas ba.
Matsalar Rashin Yarda da Gwaji: Wannan babbar matsala ce wadda a kullum ake samun yawaitar mace-mace a Kano. Mutane da yawa ba su yarda su je a gwada su ba. Wasu saboda raahin wayar da kai ne, wasu kuma ba su so a killace su, domin ba samun tallafin gwamnati za su yi ba, ballantana a ciyar da su a lokacin da su ke a killace. Akwai dalilai da dama.
Har yanzu ana mutuwa birjik a Kano
“Kawu ai mu ma mu na cikin halin jimami. Shekaranjiya wani likita ya mutu a layin mu. Kwana daya kafin nan fa lafiyar sa kalau, har ma asibiti ya je ya yi tiyata. Ya dawo da zazzafi kuma ya yi ta haki ya na kakari. Bayan kwana daya ya mutu.
“Yau kuma wani makaucin sa ya mutu, kuma yanzu haka ga wani makaucin na sa can kwance ba shi da lafiya.”
Wannan furucin wata mazauniyar Unguwa Uku cikin Kano, bayan sun gaisa a ranar Laraba, kwana biyu bayan isar tawagar Shugaban Kasa Kano.
Coronavirus ce ke kashe mutane a Kano – Dakta Yusuf Usman
Tsohon Shugaban Hukumar Inshorar Lafiya ta kasa, Yusuf Usman, ya jajairce cewa cutar Coronavirus ce ke kashe mutane a Kano ba yunwa kamar yadda wasu ke cewa ba.
A wata tattaunawa da gidan Radiyon BBC, ranar Laraba, ya musanta batun cewa jama’a na mutuwa a Kano ne saboda yunwa sakamakon dokar kulle da gwamnatin jihar ta sanya, Farfesa Usman Yusuf ya ce “me ya sa mutane ba su mutuwa a Daura ko Kaduna ko Legas ko Fatakwal? Me ya sa sai a Kano?
“Cutar Corona ce ta ke fyadar ‘ya ‘yan kadanya a jihar. Kuma dole ne a dauki mataki kafin al’amarin ya ta’azzara zuwa wasu jihohin masu makwabtaka a arewacin kasar kasancewar Kano ce mahada.”
Karancin Jami’an Lafiya A Asibitoci: Rahotanni da dama da kuma masu jiyyar marasa lafiya na kokawa da karancin jami’an lafiya, saboda kulle asibitoci masu zaman-kan su akasari. Wannan na sa marasa lafiya kan zauna a gida likitoci ko masu kemis su na rubuta musu magunguna, su na sha a gida.
Wani bincike kuma da wakilin mu ya yi a cikin jama’a ya gano cewa wasu asibitoci na gudun karbar marasa lafiya, saboda gudun daukar jangwangwama, wato mai cutar Coronavirus wanda ka iya goga musu cutar da za ta janyo a killace su, kuma ya janyo kulle asibitin.
Mutane Sun Ki Zaman Gida Sai Zaman Hira A Kofar Gidaje: Duk wasu matakan kariya da suka wajaba su rika dauka.
Rufe Kano da aka ce an yi tamkar bonono ne, wai rufe kofa da barawo. Jama’a ba su daina shiga Kano daga wasu garuruwa ba. Sannan kuma mako guda da aka yi ba a yi wa kowa gwaji ba, ya haifar da babbar matsala. A yanzu yawan wadanda aka samu da cutar sun haura 100.
Matsalar Rashin Ruwan Sama: An kusa kwanaki 40 cur ba yi ruwan sama a Kano ba. Wannan ya haddasa zafi sosai a Kano, musamman a cikin watan Afrilu.
Tallafi da tatsuniyar tallafi a Kano
Birnin Kano gari ne mai cike da milyoyin talakawa, mabukata da sauran ba’arorin marasa galihu. Yayin da gwamnati ke ta kururuwar kashe bilyan sama da 23 da ta ce ta rika tura wa marasa galihu, sai ka yi ni ka na tambayar mutane kowa na ce maka bai ma taba ganin wanda aka raba kudin ya samu ballantana shi ya samu na sa kason.
Tallafin da Gwamna Abdullahi Ganduje ya kadaddamar da rabo, na shinkafa ne tirela 10 wadanda Kwamitin Shugaban Kasa ya aika Kano, kuma a wannan makon aka sake sanarwar cewa ga wasu tireloli guda can an loda musu buhunan gero, dawa da masara sun doshi Kano.
Tallafin da Uwargidan Shugaban Kasa, Aisha Buhari ta aika, akasari na kayan aiki ne a asibitoci, kuma an ce an raba su a asibitoci daban-daban na fadin jihar.
Ko ma dai me kenan, al’ummar Kano na ci gaba da ji da ganin jama’a na wucewa da makara dauke da gawa zuwa makabartu. Mace-macen da Fadar Shugaban Kasa ta ce ana binciken gano musabbabin su.
Discussion about this post