Gwamnatin Kaduna ta kara kwana daya, bayan janye ranar Talata da ta yi a shekaranjiya.
Yanzu za a rika samun walwala duk ranar Laraba da Asabar. Mutane zasu garzaya Kasuwa su siya abinci sannan su koma gida.
Hakan na kunshe a wani sanarwa da gwamnatin ta saka a shafin ta Tiwita.
Yin haka sassauci ne daga dokar da gwamnatin jihar ta saka na soke ranar Talata a matsayin ranar walwala a jihar.
Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana sanar da kara kwanaki 30 daga ranar Litini na ‘Zaman Gida Dole’ da hana walwala a jihar Kaduna.
Sanarwar haka ta fita daga bakin Kakaikn gwamnatin jihar Muyiwa Adekeye wadda shine ya saka wa takardar hannu a madadin gwamna el-Rufai.
” Ganin yadda ake ta samun karuwar yawan wadanda suka kamu da cutar a musamman babban Birnin Tarayya, Abuja, sannan kuma da tabbaci da aka samu cewa tafiye-tafiye a tsakanin jihohin dake zagaye da jihar na yada cutar, kwamitin ta bada shawarar a tsaurara matakai don kare mutanen jihar.
” Gwamna El-Rufai ya amince bayan an duba rahotan yadda dokar garkame mutane ya gudana a Kaduna, daga wannan mako sau daya za a rika fita zuwa kasuwanni da dan walwala. Am bada ranar Laraba a matsayin wannan rana, gwamnati ta soke ranar Talata.
” Daga yanzu ranar Laraba ne kawai za arika fita, har sai an samu sahihan bayanai na an iya kakkabe wannan cuta.
” Sannan kuma duk wanda zai fita daga gidan sa daga yanzu sai ya saka takunkumin fuska dole kuma ayi nesa-nesa da juna a kasuwanni da zaman cikin mota. Gwamnati za ta wadata gajiyayyu, da wadanda basu da halin siya da takunkumin fuska. Bayan haka an yi kira ga mutane su garzaya ga tailoli su dinka musu takunkumin da za su iya wanke wa idan yayi datti.
” Dole a saka takunkumin fuska a fadin jihar, domin kare kai daga kamuwa da cutar.
1 – Dole kowa ya zauna a gida dole
2 – Ba a yarda a bude ofisoshi ba, Kasuwanni, wuraren shakatawa, shaguna, masallatai da coci-coci, wato wuraren bauta.
Wadanda aka yardarwa su ci gaba da zirga-zirga sune ma’aikatan kiwon lafiya, ma’aikatan Kashe gobara, ma’aikatan albarkatun ruwa da wutan lantarki sannan kuma da jami’an tsaro. haka kuma tankoki dake kai mai gidajen saida mai.
Discussion about this post