Ni ma na kamu da Coronavirus, na tafi Gwagwalada sai na dawo – Inji Dokpesi,

0

Shugaban rukunin Kamfanonin ‘DAAR Kwaminikeshon’, kuma dan fitaccen dan jarida kuma dan siyasa, Raymond Dokpesi ya kamu da cutar coronavirus.

Dokpesi da kan sa ya bayyana haka a wani sako da ya aika wa ma’aikatansa inda ya ce ya kamu da cutar coronavirus, kuma yanzu ya tattara kayansa zai koma asibitin Gwagwalada, inda ake duba marasa lafiya.

Ya ce an yi wa iyalan sa gwajin cutar basu da ita.

Ya yi kira ga ma’aikatan sa da suka yi cudanya a kafin cutar ta bayyana a jikin sa da su garzaya a duba su.

Har yanzu ba a san inda Dokpesi ya kamu da wannan cuta ba, domin bai yi tafiya zuwa kasar waje a tsawon lokaci.

Yanzu dai ya shiga cikin jerin manyan ‘yan Najeriya da suka kamu da cutar a kasar nan.

Share.

game da Author