‘Yan sanda sun damke masu garkuwa da mutane, fyade da ‘yan fashi 71 a jihar Adamawa

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta kama masu garkuwa da mutane,fyade da ‘yan fashi da makami 71 a bangarori daban daban a jihar.

Kwamishinan ‘yan sanda Audu Madaki ya sanar da haka a taron manema labarai da aka yi ranar Talata a garin Yola.

Madaki yace 11 daga cikin mutanen da suka kama sun yi saranda a gaban kungiyar Miyetti Allah wanda kungiyar ta danka su a hannun jami’an tsaro.

Ya ce sun kama manyan bindigogi kirar AK47 guda 13, tsabar harsashi 761, wasu bindigogin guda biyar, adda 12, wukake takwas da daurin miyagun kwayoyi da dama.

“ Daga cikin mutanen hudu masu yi wa mata fyade ne, ‘yan fashi 51 sauran kuma masu ta’ammali da miyagun kwayoyi da ta’addanci ne.

Ya yi kira ga mutane da su taimaka wajen bada bayanan da za su taimaka wa jami’an tsaro wajen ganin sun hana miyagun aiyukka a jihar.

Idan ba a manta ba a watan Fabrairu, rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ita ma ta shaida cewa jami’anta sun kashe mahara 17 sannan sun kwato dabbobi 189 a karamar hukumar Kankara.

A kauyen maharan sun yi bata kashi da kungiyar ‘yan banga inda har suka kashe mutane 4 sannan sun kwashe dabbobin mutane da dama.

Share.

game da Author