Farashin danyen man fetur ya karye warwas da kashe 30 bisa 100 a duniya, wanda hakan ya haifar wa Najeriya gagarimar matsalar samun kudaden shigar gudanar da ayyukan kasafin kudi.
Bayanai sun tabbatar da cewa a yau danyen mai ya koma ganga daya a kan dala 35.42, ya zuwa ranar Litinin da safe.
Cikin watan Disamba ne Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudi na 2020 na naira tiriliyan 10.50.
An yi wannan kasafin makudan kudade ne a kan kirdadon da Gwamnatin Tarayya ta yi cewa a kullum za ta rika hako danyen mai har ganga milyan 2.18, a kan farashin danyen man fetur dala 57 a kowace ganga.
A yanzu Najeriya ta fuskanci babbar matsalar karancin kudaden shiga sakamakon karyewar farashin danyen man fetur, ta yadda ba za a iya aiwatar da wasu muhimman ayyukan raya kasa da ke cikin kasafin 2020 ba.
Barkewar Coronavirus ya haifar da nakasu da tawaya ga tattalin arziki a duniya baki daya.
Idan ba a manta ba, Kasuwar Hada-hadar Hannayen Jari ta yi karyewar da ta samu asarar kusan naira bilyan 350 a wannan mako.
Dama kuma ita ma Kasuwar Hada-hadar Hannayen Jari da bazar farashin danyen mai a duniya ta ke fankama. Tunda kuma farashin ya karye a duniya, to tilas ya shafi Najeriya ita ma.
Gwamnati Ba Za Ta Iya Wasu Ayyukan Cikin Kasafin 2020 Ba – Ministar Kudi
Ministar Harkokin Kudade, Zainab Ahmed ta bayyana cewa za a zabtare kasafin 2020, domin a yi daidai iyar ‘yan kudaden shigar da ke shigo wa gwamnatin tsarayya kawai.
Amma har yanzu ba a sani ba ko bangarorin da gwamnati za ta zabge kudaden da ta yi niyyar kashewa a kasafin 2020. Za su shafi fannin lafiya, ilmi, ayyukan noma da kuma wutar lantarki.
Dama tun bayan gabatar da kasafin 2020, ‘yan Najeriya suka rika karafin cewa kudaden da Buhari ya rubuta zai kashe a wadannan fannoni na sama, sun yi kadan matuka.
Coronavirus ta zama gobarar da ta mamaye duniya, kamar yadda wani masanin tattalin arziki mai suna Paul Alaje ya bayyana.
Ya ce Coronavirus ba a kan mutane kadai ta tsaya ba, ta ma zama wata gobara mai kone tattalin arzikin kasashe.
Paul ya ce idan ba a gaggauta shawo kan wannan mummunar cut aba, to za ta karya tattalin arzikin dinuya, kasashe su karye saisai, kuma manyan kasashe su yi ragas tare da kanana.
Najeriya na fuskantar barazanar faduwar farashin danyen mai a duniya, a cikin gida kuma ta na fama da karancin tara kudaden haraji.
MAFITA: Ko A Zabge Kasafin Kudin 2020, Ko A Kara Ciwo Tulin Bashi
Masanin tattalin arziki Paul ya ce a yanzu dai mafita biyu ne suka rage wa Najeriya, kuma duk marasa dadin sha’ani.
“Ko dai gwamnatin Najeriya ta zabge kasafin kudin 2020, domin a haka dai wasu dimbin ayyukan da aka yi alkawari ba za su yiwu ba, ko kuma a kara ciwo bashi a lafta a kan tulin wanda aka jajibo a baya da kuma na baya-bayan nan.”
Ya ce idan aka kuskura kuma aka kara ciwo bashi, to dan abin da Najeriya ke samu a duk karshen wata zai rika tafiya wajen biyan basussuka.