‘Yan bindiga sun bindige jami’an tsaron Najeriya su 29 a cikin Karamar Hukumar Shiroro, Jihar Neja.
Jami’an da aka kashe din gamin-gambiza ne daga sojoji, ‘yan sanda da kuma ‘Yan sintiri da aka kafa domin fatattakar mahara a yankin.
Wannan lamari ya faru a cikin Dajin Galkogo da ke Karamar Hukumar Shiroro, inda su ma maharan aka kashe masu yawa a cikin su.
Kisan wanda ya faru a ranar Lahadi da ta gabata, ya faru ne a rana daya da kusan da Boko Haram suka yi wa sojojin atileri 50 a hanyar Alargamo, cikin Jihar Yobe, a yankin Arewa maso Gabas.
Rahotanni sun tabbatar da ganin yadda aka kwashi gawarwakin jami’an tsaro 29 da aka kashe a Shiroro, aka kai su Babban Asibitin Minna, babban birnin Jihar Neja.
Kwana daya dama kafin wannan mummunan kisan, mahara sun kai farmaki a kauyukan Galkogo da Zumba da ke Shiroro.
Da PREMIUM TIMES ta nemi jin ta bakin Kakakin Yada Labarai na ‘Yan Sandan Minna, Wadiu Abiodun, sai ya ce ba zai yi magana ba, domin akwai sojoji a cikin lamarin.
An tuntubi kakakin sojojin Najeriya, Sagir Musa, shi ma sai ya ce a tuntubi Daraktan Riko na Yada Labaran Sojojin Ayyukan Musamman, John Eneuche, wanda aka tura wa sakon tes, amma bai maida amsa ba, har zuwa lokacin da aka rubuta wannan labari.