Gwamnatin Jihar Kano ta bada umarnin cewa dukkan malaman makarantun allo da na tsangayu su rufe, a maida kowane almajiri gidan iyayen sa.
Wannan umarni ya biyo bayan wani taron gaggawa da Sakataren Gwamnatin Jiha, Usman Alhaji ya yi tare da Ma’aikatar Ilmi da kuma Shugabannin Makarantun Tsangaya su 50 a Gidan Gwamnati.
Sanarwar ta ce an fito da wanaan tsarin a cikin gaggawa ne domin a rage cinkoson jama’a, yadda za a samu saukin dakile yaduwar cutar Coronavirus a fadin jihar.
Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ne ya bada wannan umarni, ta hannun Sakataren Gwamnati, Usman Alhaji cewa kowane malamin makarantar allo ya tabbatar da ya sallami dukkan almajiran da ke karkashin sa, sun koma gidan iyayen su, a jihar da kowane ya fito.
Idan ba a manta ba, a ranar Litinin ne gwamnatin jihar Kano ta rufe dukkan makarantun jihar. Kuma ta na ci gaba da daukar wasu kwararan matakai domin hana yaduwar Coronavirus, a birni mafi yawan al’umma a kasar nan, in banda Legas.
Gwamnatin Jihar Kano ta hana harmutsa fasinjoji dankam cikin manyan motoci ana shiga da su Kano, saboda gudun kamuwa da Coronavirus.
Sanarwar da Kwamishinan Yada Labarai Muhammad Garba ya saw a hannu, ranar Talata, ta bayana cewa sai wadanda ke gudanar da ayyukan musamman ne kadai aka dauke wa umarnin tsayawa gidajen su.
Kwamishinan ya kara bayyana cewa majalisa ta amince da matakan da aka dauka domin hana barkewar yaduwar cutar Coronavirus a Kano, birni na biyun yawan jama’a a Najeriya.
Hana Bas-bas makare mota da fasinjoji
Garba ya ce har yau dai ba a samu ko da rahoton mutum daya da ya kamu da cutar a Kano gaba dayan jihar ba. amma dai ana daukar matakan ne domin hana barkewar annoba.
Don haka an hana shiga Kano da lodin fasinjoji dankam a cikin manyan motoci.
Ya ce akwai hadari sosai a irin lodin da ake yi wa manyan motocin bas-bas, inda ake loda musu jama’a a cunkushe.
“Gwamnatin Jihar na aiki ba dare ba rana domin tabbatar da cewa wannan cuta ta Coronavirus ba ta shiga jihar ba. Ko ma ta shiga, to ana kokarin ganin an dakile ta daga barkewa.” Inji sanarwar.
Daga nan ya shawarci jama’a a bi dokar gwamnati kuma a bi ka’idojin da hukumomin lafiya suka gindaya.
A jihar Bayelsa kuma an hana motocin taksi daukar fiye da fasinjoji biyu a baya. Sannan kuma an umarci direbobin su dauki fasinja daya kawai a gaba.