Shugaban Hukumar Shige da Fice ta Kasa, Mohammed Babandede ya bayyana cewa gwaji ya bayyana cewa ya kamu da cutar coronavirus shima. Babandede ya ce tun bayan dawowar sa daga kasar Birtaniya ya Killace kan sa kafin ma a yi masa gwajin. Sakamakon gwajin ya nuna cewa ya kamu da cutar.
Sai dai kuma duk da cewa Babandede ya yi wannan tafiya da matan sa ne, ita ba ta da cutar.
Haka shima shugaban Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ibadan, Jesse Otegbayo, ya kamu da cutar.
Sai dai Otegbayo ya ce shi ba daga kasar waje ya samo cutar ba.
Muna mitin ne da wasu manyan ma’aikata a dakin taro sai daya daga cikin mu ya fara nuna alamun rashin lafiya.
Daga nan ne fa sai muka watse aka kai shi asibiti. Bayan an tabbatar yana dauke da cutar sai naje na yi gwaji. Sakamakon gwajin ya tabbatar nima na kamu da cutar.
” Tun bayan haka na umarci duka wadanda suka halarci wannan taruka da muka rika yi har zuwa wannan rana da su killace kan su kafin ayi musu gwaji. Wannan cuta da gaske ta ke yi saboda haka ina kira gareku da ku kaurace wa yawan cudanya da juna. Muddun kuka ga ko ji ba daidai ba toh, ku gaggauta garzayawa asibiti a duba ku sannan a killace kai da wuri wuri.