Mahara a bisa dawakai 10 sun sace mahaifiyar shugaban al’umma a Jigawa

0

A wani sabon salon yin garkuwa da mutane da ya bullo a jihar Jigawa, wasu mahara a bisa dawakai sun farwa garin Takanebu, karamar hukumar Miga, inda suka arce da mahaifiyar wani attajiri kuma shugaban al’umma.

Maharan sun sun rika sukuwa tun daga kungurmin daji rataye da bindigogi sannan suka afka wa wannan gida. Sun buka ci a mika musu Harira Nasir,mahaifiyar Abdulkarim Nasir.

kakakin ‘Yan sandan Jihar Jigawa Audu Jinjiri ya tabbatar da aukuwar wannan abu, inda ya kara da cewa tuni har an aika da jami’ai su fantsama wajen damko wadanda suka aikata wannan abun tashin hankali.

Wani da abin ya faru a gaban sa ya shaida cewa maharan sun bukaci su mika Harira. ” Ganin suna dauke da bindigogi sai muka fito da ita daga cikin daki muka mika ta.

Daga nan sai suka dora ta bisa doki suka ci gaba da sukuwa zuwa inda suka fito. Kuma har yanzu basu tuntubi ‘yan uwa ba tukunna.

Maharan sun kai su goma akan dawakai.

Jihar Jigawa, Kaduna da Katsina sun yi kaurin suna wajen ayyukan mahara da masu garkuwa da mutane.

Ita ma Jihar Zamfara, tana fama da irin wannan hare-hare da tashin tashina a yankunan ta da dama.

Share.

game da Author