Yadda matafiya ya ci zarafin malaman asibiti saboda sun matsa sai ya killace kansa

0

Wani matafiyi da ya dawo daga kasar Ingila ya ci zarafin wasu malaman asibiti a dalilin tilasta masa da suka yi ya killace kan sa.

Shi dai wannan matafiyi ya ki tsayawa a duba shi sannan da aka umarce shi ya killace kansa ya yi musu tsiwa ya kama gaban sa.

Daga nan sai wuce kai tsaye zuwa jihar Delta in da nan ne asalin sa.

Duk da haka ma’aikatan lafiya ba su hakura ba. Sai suka bi shi zuwa can.

Da suka isa gidan sa sai suka buja ci a yi musu sallama da shi.

Fitowar sa ke da wuya sai ya bi su da fada, yana ta zage zage kuma ya fatattake su daga gidan sa.

Bai kyale su haka nan ba sai ya bisu tare da da wasu ‘yan banga zu ka ci zarafin ma’aikatan.

Daga baya sai da kwamishinan lafiya na jihar Delta Mordi Ononye ya sa baki a wannan magana inda ya nemi wannan mutum ya bi doka da umarnin ma’aikatan lafiya tunda ya dawo daga kasar da mutane suka kamu da cutar coronavirus ne.

Sannan wannan mutum ya ce yadda ma’aikatan suka rika yi masa ne ya bashi haushi. Amma kuma ya roke su yafe masa abin da yayi musu.

Share.

game da Author