Kotu ta dakatar da Oshiomhole daga shugabancin APC

0

Babbar Kotun Tarayya da ke Jabi, Abuja, ta umarci Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Adams Oshiomhole ya daina kiran kan sa shugaban jam’iyyar, saboda ta dakatar da shi.

Sannan kuma kotu ta ce kada a bar Oshiomhole ya sake shiga sakateriyar jam’iyya ta kasa.

Mai Shari’a Danlami Senchi, ya bada umarnin dakatarwar bayan da ya saurari wani korafi da aka gabatar a kan Oshiomhole, cewa tunda an dakatar da shi a cikin APC a Jihar sa ta Edo, to babu wani dalilin da zai sa ya ci gaba da zama shugaban APC na Kasa kuma.

Wani mai suna Oluwale Afolabi ne ya shigar da karar a ranar Laraba. Ya hada da Oshiomhole da kuma jam’iyyar APC ita kan ta duk ya maka su kotu.

Afolabi dai ya shigar da wannan kara ce tun a ranar 16 Ga Janairu, inda ya ce an dakatar da Oshiomhole daga cikin jam’iyyar APC a jihar Edo, kuma har zuwa yau bai kalubalanci dakatarwar da aka yi masa a kotu ba.

Don haka mai kara ya ce tunda Oshiomhole bai yi tankiyar dakatar da shi ba ta hanyar kalubalanta a kotu, saboda haka bai cancanta ya ci gaba da zama shugaban jam’iyya na kasa ba.

Wani babban lauya mai suna Damian Dodo ne lauyan da Oshiomhole da APC suka dauka.

Mai Shari’a Senchi a ranar Laraba ya ce kuskure ne Oshiomhole ya rika kira kan sa shugaban APC, sannan ita APC din kuskure ne ta ci gaba da rike shi a matsayin shugaban ta na kasa, tunda a mazabar sa, wato jihar Edo an dakatar da shi.

“Daga yau kada ka kara kiran kan ka shugaban APC na kasa, kuma kada ka sake amsawa idan aka kira ka shugaban APC na kasa, har sai bayan abin da hukuncin kotu ya zartas.”

Mai Sahri’a ya kuma umarci APC ka ta sake ta kara kiran Oshiomhole da suna ko lakabin shugaban ta na kasa.

Sannan kuma kotu ta ce kada a bar Oshiomhole ya sake shiga sakateriyar jam’iyya ta kasa.

Share.

game da Author