SABON ZARGI: Majalisar Kano za ta binciki Sarkin Kano Sanusi

0

Majalisar Kano za ta sake bincikar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi, a bisa wasu korafe-korafe da wasu mazauna jihar suka mika gaban ta, suna zargin Sarki Sanusi da ci wa al’adun Kano fuska.

Shugaban kwamitin kananan hukumomi da masarautu na majalisar Zubairu Hamza-Masu ya bayyana a zauren majalisar cewa kwamitin ta karbi korafi guda biyu, daya daga Muhammad Mukhtar, na biyun kuma daga shugaban hukumar KSPCE, Muhammad Bello-Abdullahi, duk sun zargin sarki Sanusi da banzatar da al’adun mutanen jihar da kuma rashin daraja masarautar Kano.

Dan majalaisa Hamza ya ce dukka wadannan mutane biyu na rokon majalisar ta yi zurfin bincike akan wannan zargi da korafi da suka mika gabanta.

Shugaban majalisar dokokin jihar Abdulaziz Gafasa ya mika wannan korafi ga kwamitin majalisar ta yi bincike nan da sati daya.

Idan ba a manta ba, gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje da Sarki Sanusi sun saka kafar wando daya tun bayan zaben 2019 inda a yanzu haka basu ga maciji a tsakanin su.

A dalilin haka wasu ke ganin yasa gwamna Ganduje ya kirkiro sabbin masarautu har hudu a jihar domin rage karfin Sanusi a Kano.

Rashin jituwar ta kai ga saida kungiyar dattawan jihar Kano suka saka baki amma ba a samu maslaha ba.

Shima shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce ba zai ce komai ba akai duk da mutane sun nemi ya shiga tsakanin gwamna Ganduje da Sarki Sanusi.

” Ba zan ce komai akan rashin jituwan dake tsakanin Ganduje da Sarkin Kano ba saboda abu ne na jiha kuma majalisar dokokin jihar na bindiddigin abin.” Inji Buhari.

Share.

game da Author