Gwamnatin Amurka ta bada tabbacin biyan dala milyan 7, wato kwatankwacin naira bilyan 2.5 ga duk wanda ya bayar da bayanan da suka yi sanadiyyar damke shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau.
Gwamnatin ce ta yi wannan sanarwar a ranar Laraba a shafin Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka na twitter aka yi wannan sanarwa.
“ Ma’aikatar Kula da Harkokin Kasashen Waje ta Amurka za ta biya naira milyan 7 Ga duk wani wanda ya bayar da bayani sahihi wanda zai iya kai ga damke Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau.
Baya ga rubuta bayanin da Turancin Ingilishi, an kuma yi bayani da harshen Turancin Faransa.
Shekau ya kama ragamar shugabancin Boko Haram, tun bayan kashe tsohon shugaban kungiyar, Mohammed Yusuf.
Duniya ta raja’a a kan Shekau cikin 2014, bayan ya yi garkuwa da daliban sakandaren mata sama da 300 daga Chibok, cikin Jihar Barno.
Wannan ne ya haifar da taratsin #BringBackOurGirls, wanda ya game duniya kamar ruwan dare. Cikin wadanda suka rika yayata wannan rokon neman dawo da daliban kuwa har da Michelle Obama, matar tsohon shugaban Amurka, Barack Obama.
“Ni na sace ‘yan matan ku, kuma zan sayar da su a kasuwa. Wallahi kuma duk zan aurad da su a tsakanin mu.” Haka Shekau ya fada a lokacin da ya ke tabbatar da cewa su suka yi garkuwa da matan.
Dama cikin watan Yuni, 2012 Amurka ta taba sa ladar dala milyan 7 bga duk wanda ya fallasa yadda za a iya kama Shekau.
Daga 2009 zuwa 2019, Boko Haram sun kashe mutane sama da 35,000 tsakanin Arewa maso Gabas, jihohin Barno, Yobe da Adamawa.