An sauke lodin wasu tubabbun Boko Haram a Maiduguri, bayan sarandar da suka yi a hannun sojojin Jamhuriyar Nijar.
Tubabbun Boko Haram din dai an sauke su a filin jirgin sama na Maiduguri daga wani jirgin yakin sojojin sama, a cikin rakiyar wasu manyan sojoji a karkashin Manjo Janar Bamidele Shafa.
Janar Shafa shi ne Shugaban Shirin Gwamnatin Tarayya na Karbar Tubabbun Boko Haram.
Shafa ya bayyana cewa, “yanzu muka sauke lodin wasu tubabbun Boko Haram su 25, da suka hada da maza, mata da kuma kananan yara ‘ya’yan su.”
Ya ce tubabbun Boko Haram din sun ajiye makaman su suka yi saranda a hannun sojojin Jamhuriyar Nijar. Su kuma na Nijar suka tuntubi sojojin Najeriya domin a kwason su, a maido su gida.
“Don haka mun kwaso su lafiya, mun maido su gida lafiya, kuma mun damka su a hannun Gwamnatin Jihar Barno, domin a ci gaba da shirin saisaita rayuwar su da yi musu wankin kwakwalwa domin kankare musu mummunar akidar da Boko Haram ta cusa musu.”
“To mu na amfani da wannan dama domin kara yin kira ga wadanda ke jeji sun a hare-hare, su fito su karbi tayin Shugaban Kasa domin su yi saranda, a yi musu afuwa, don a samu zaman lafiya.”
Kwamishinar Harkokin Mata ta Jihar Barno, Zuwaira Gambo ce ta karbi tubabbun Boko Haram din.
Ta bayyana cewa Gwamnatin Jihar Barno za ta samar musu tallafin ciyarwa, shayarwa, tufafi, za su samar musu ilmi bakin gwargwado, tare kuma da koya musu sana’o’in hannu.”
Ta ce akwai cibiyar da ake gudanar da irin wannan shirye-shirye, wadda Gwamna Babagana Zulum ya wadata da isassun kayan koyon aikin sana’o’in hannu.
“Za a koya musu wadannan sana’o’i sannan sai a sallame su kowa a hada shi da iyayen sa.” inji Kwamishina Zuwaira.