Wasu mazauna sansanin gudun hijira a sansanoni biyu sun yi zanga-zanga a ranar Laraba, inda suka cika garin Yola sun a nuna rashin amincewa da karancin abincin da ba su samu daga gwamnatin tarayya.
Masu zanga-zangar sun yi korafin cewa watanni hudu kenan su na fama da karancin abinci.
Masu zanga-zangar sun yi cincirindo a Dandalin Muhammadu Ribadu, a Jimeta, Yola.
Sun bayyana cewa rabon da su samu tattafin abinci daga Hukumar Agajin Gaggawa ta Kasa NEMA, an kai watanni hudu.
Wakilan masu zanga-zangar dai sun isa Yola tun daga sansanonin su da ke Fufore, suka ce kusa mazauna sansanin gudun hijira su 1,000 ke zaune a sansanin.
Kakakin su Umar Bakura, ya ce, “Daga wata hudu da suka shude zuwa yau, ba mu samu gudunmawar abinci daga Gwamnatin tarayya ko da lomar tuwo daya ba. Babu abin da NEMA ta aiko ko ta kawo mana. A cikin mu kuwa akwai kananan yara, dattawa da kuma marayu.
“Mu na kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya shigo lamarin. Idan ba za a tattafa mana da abinci ba, to a zo a maida mu kananan hukumomin da muka baro a jihar Barno.” Inji Umar.
Umar ya ce shi da wasu sun sha kai kukan su ga NEMA, amma aka yi biris da su.
Ya ce dukkan mazauna sansanonin Fufore da ke cikin Jihar Adamawa, daga cikin kananan hukumomin jihar Barno ne Boko Haram suka tarwatsa su, suka tsallaka gudun hijira a jihar Adamawa.
‘Karya Su Ke Yi, Mun Kai Musu Abinci A Watan Disamba – NEMA
Shugaban Gudanar da Ayyukan NEMA a Jihar Adamawa da Taraba, Midala Anuhu, ya karyata zargin da masu zanga-zangar suka yi wa NEMA, inda ya ce an kai musu dauke a cikin watan Disamba, 2019.
“Mun tura korafe-korafen su a hedikwatar NEMA da ke Abuja, kuma jiran a aiko da abincin daga can mu ke yi. Da an turo, mu kuma za mu raba musu.”Inji Nuhu.