Ba Chelsea ce aka fara bi har gida aka dankara wa kwallaye 3 ba. Sannan kuma ba Real Madrid ce ta aka fara kunyatawa a gaban magoya bayan ta kusan 95,000 ba. Amma dai abin da ya faru da su biyun a ranakun Talata da Laraba, ya nuna cewa Bayern Munich da Manchester City sun sakar musu sukuntumau, ko kuma rauhanai a wasannin farko na zagaye na biyu na cikin Kofin Zakarun Turai.
Sai kociya Frank Lampard da Zinadine Zidane sun tsayin daka sun yi tashin tsayuwar-dare sun a girka, kafin su cire wa Chelsea da Madrid rauhanan da aka bi su har gida aka saki a kan su.
Dukkan kungiyoyin Jamus da ke cikin gasar, ba wanda bai yi nasara a wasan san a farko na zagaye na biyu ba. Beryern Munich ta ci Chelsea a filin ta na Stamford Bridge 0:3.
Brussia Dortmund ta ci PSG 2:1, ita kuma Leipzig ta lika a Tottonham kwallo daya 1:0 a birnin London, Ingila.
Ko a Gasar UEROPA ma kungiyoyin Jamus kowace ta ci wasan ta na zagaye na biyu: Bayer Leverkusen ta ci FC Porto 2:1, Entracht Frankfurt ta ci RB Salzburg 4:1, yayin da Wolfsburg ta yi nasara a kan Malmo da ci 2:1.
A Faransa kuwa FC Lyon ta lika wa Juvestus 1:0, an su Ronaldo na cizon yatsa. Barcelona ta kwaci kanta a hannun Napoli da ci 1:1. Ita kuwa Liverpool tun a wancan makon aka tika bugu daya mai ban-haushi a hannun Atletico Madrid, a Spain.
Korar dan wasan bayan Madrid, Sergio Ramos da aka yi, an kara kwanto wa Madrid kura a karawar da za ta yi ta biyu da Manchester City.
Dama ga shi kuma har yau ba a fara maida uwar kudi ba, ballantana a kai ga maganar ribar sayen Eden Hazard da Madrid ta yi daga Chelsea. Tun da ya zo ya ke fama da jin ciwo, kuma yawancin wasannin da aka yi nasara a kan Madrid, ya na ciki.
Ba abin mamaki ba ne idan Madrid ta kwaci kan ta a hannun Manchester City a karawa ta biyu. Domin hakan ta faru kan Barcelona sau biyu, bayan ta lallasa Roma da Liverpool da kwallaye uku. Amma a wasa na gaba duk sai da suka yi gabata a kan Barcelona.
Zai yi wuya Chelsea ta rama kwallaye 3 da Bayern ta zabga musu. Amma dai baa bin mamaki ba ne idan ta rama.