Majalisar dattawa ta kirkiro kudiri don kafa hukumar tubabbabun ‘yan Boko Haram

0

Majalisar dattawa ta kirkiro kudiri don kafa hukumar tubabbun ‘yan Boko Haram.

Sanata Ibrahim Geidam dake wakiltar Yobe ta Gabas ya karanta manufar wannan kudiri a zauren majalisar ranar Alhamis.

An karanta kudirin a karo na farko.

Sai dai kuma ba tun yanzu ba wasu da dama daga cikin manyan jihar Barno da Yobe sun kushe wannan manufa tun a baya, inda suka koka cewa ba lallai bane wadanda suka mika wuya daga cikin ‘yan Boko Haram sun tuba ne.

Tun a wancan lokacin wanda tsohon gwamna Kashim Shettima ya jagoranci dattawan wajen kira ga sojoji da su rika sara suna duban bakin gatari.

A watan jiya, Sojoji sun yi ikirarin cewa akwai ‘yan Boko Haram sama da 600 da suka tuba, suna wani sansani a Jihar Gombe ana horas dasu da yi musu wankan tsarki.

A wancan lokacin sun koka cewa idan ba amaida hankali maimakon a gyara sai a rugurguza ci gaban da aka samu diomin kila turo su akayi su riki aika wa kungiyan bayanan sirri a boye.

Daga nan sai suka yi kira ga gwamnati tun a lokacin da ta yi watsi da wannan shiru tukunna har sai ta tantance sannan ta tabbatar na kwarai ne suka tuba cin su.

Share.

game da Author