Sai an kara daukar sojojin 100,000 za a iya murkushe Boko Haram -Zulum

0

Gwamna Babagana Zulum na Jihar Barno, ya ce kafin a ga bayan Boko Haram sai an kara daukar akalla matasa 100,000 aikin soja.

Ya ce idan har Shugaban Kasa ya amince a kara dauka, to jihar sa zai iya samar da sojoji 50,000.

Daga nan sai ya yi kira da a sake yi wa Dokar Daukar Aikin Soja kwaskwarima, yadda za a yi gaggawar daukar karin sojoji masu yawa, domin a yi wa Boko Haram taron dangin ganawa don kawar da ta’addanci.

Zulum ya yi wannan jawabi ne a gaban Kwamitin Majalisar Tarayya mai kula da Harkokin Tsaro, da suka kai masa ziyarar ganin halin da Jihar Barno ke ciki kan matsalar tsaro.

Gwamnan ya yi wannan bayani, kwanaki kadan bayan Shugaban Kwamitin Tsaro na Majalisar Dattawa, Ali Ndume, ya bayyana cikin wata hira da Talbijin na Channels cewa a gaskiya sojojin da ke yaki da Boko Haram a Arewa maso Gabas.

Zulum ya kara yin bayanin cewa akwai karancin sojoji, karancin makamai da karanci kayan na’urorin fasahar yankin zamani a sojojin Najeriya.

Sai ya roki Shugaban Kwamiti, Honorabul Babajimi Benson, ya ce ya shaida wa Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawal ya sanar da Shugaba Muhammadu Buhari a gyara dokar daukar sojoji domin a gaggauta daukar zarata akalla 100,000.

Bukatar sake daukar sojoji 100,000 ta zo kwana daya bayan PREMIUM TIMES ta buga tattaunawa da tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya. Babachir Lawal, wanda ya ce zamanin yakin gaba-da-gaba tsakanin kato da kato ya wuce

Lawal ya ce yanzu da fasahar zamani sojoji ke kai hari, kuma su yi galaba.

Share.

game da Author