YOBE: Kiristocin sun yi jimamin cikar Leah Sharibu shekaru biyu hannun Boko Haram

0

Kungiyar Kiristoci ta Kasa (CAN), reshen Jihar Yobe, ta gudanar da tattakin lumana, addu’o’i da alhinin rabuwa da Leah Sheribu tsawon shekara biyu.

Sharibu na cikin ‘yan matan Sakandaren Koyon Fasasha ta Dapchi sama da 100 wadanda Boko Haram suka arce da su a ranar 19 Ga Fabrairu, 2018 a Jihar Yobe.

An sako dukkan sauran bayan tattaunawa da gwamnatin tarayya a ranar 21 Ga Maris, 2018, amma suka rike Sharibu.

Kawayen ta da aka sako sun ce an tsare ta an ki sakin ta saboda an yi mata tayin shiga addinin musulunci, amma ta ki amincewa.

Ranar Laraba da ta kasance 19 Ga Fabrairu, ranar ce ta cika shekaru biyu a hannun Boko Haram.

Hakan ta sa CAN reshen Yobe shirya gagarimin taron tunawa da kuma bakin cikin kadaicin rashin Sheribu da suke yi.

An yi gagarimin taro a hedikwatar Cocin ECWA na jihar, aka yi addu’o’i, jimami da alhini.

An kuma yi hudubobi da jawaban kwarin gwuiwa ga Sheribu tare da addu’ar Allah ya kubutar da ita.

An kuma jinjina wa karfin halin ta, tare da yin bayanin cewa su na tare da ita duk ma irin halin da ta ke ciki.

Daga Cocin ECWA, an yi jerin gwanon tattakin lumana tare da daliban makarantu zuwa Cocin St. Mary duk a Damaturu.

An kuma yi addu’a ga Shugaban Kungiyar Kiristoci na Karamar Hukumar Michika, Bitrus Zakka da Boko Haram suka kashe cikin watan Janairu.

Shugaban CAN na jihar Yobe, Philibus Yakubu, ya jawo ayoyi daga cikin bebul tare da nuna alhini da jimami da kuma addu’o’i.

Share.

game da Author