” Ku tashi ku nemi na kan ku, ku daina jiran aikin gwamnati” -Shawarar Minista ga matasa

0

An shawarci matasan kasar nan su tashi su samar wa kan su ayyukan rufin asiri, su daina yin zaman jiran-gawon-shanun neman aikin gwamnati.

Ministan Kwadago da Ayyuka, Chris Ngige ne ya yi wannan kira a Taron Zaburar da Matasa Neman Tudun Dafawa da aka shirya a Benin, babban birnin Jihar Edo.

Ngige ya ce ayyukan kirkire-kirkire, kere-kere, kwankwashe-kwankwashe da sassake-sassake na zamani sun fi aikin gwamnati kawo kudi ga matasa.

Ya ce maimakon matasan da suka kammala digiri su tsaya jiran aikin gwamnati, ya fi dacewa su rungumi dahir, wasu ayyukan fasahar zamani da sauran ayyuka na dogaro da kai.

“Ku duba ku gani, matasan da suka fi dukkan matasan duniya kudi, wadanda ‘yan shekara 21 zuwa 31 ne, ba ma’aikatan gwamnatin kasar su ba ne, gumin su suke ci.”

Cikin sanarwar da Kakakin Yada Labarai na Ma’aikatar Kwadago, Charles Akpan ya fitar, ya ce Daraktar Ayyukan Musamman ce, Martina Nwordu ta wakilci Minista Ngige a wurin taron.

Taron dai an shirya za a gudanar da shi a sauran shiyyoyin kasar nan hudu, ta yadda za a bi ana zaburar da matasan da suka yi karatu har zuwa digiri su rungumi ayyukan inganta rayuwar su, ba tare da jiran sai ranar da suka samu aikin gwamnatin tarayya ba.

Ngige ya tunatar da cewa ta wadannan hanyoyi ne za a kara wa ayyukan samun yi kandagarkin zama abin dogaro, musamman idan aka yi la’akari da alwashin da Shuhaba Buhari ya sha, cewa zai fitar da mutum milyan 100 daga cikin kangin talauci a shekara 10.

Idan ba a manta ba, shekaru biyu bayan kama mulki, Buhari ya sha tsangwama a lokacin da ya yi wani furuci cewa matasan Najeriya sangartattu ne.

An yi ta caccakar sa, an tuna masa alkawarin da ya dauka kafin zaben 2015, na samar wa matasa aikin yi idan ya hau mulki.

Share.

game da Author