ZAZZABIN LASSA: Mutane 70 sun rasu a Najeriya – NCDC

0

Hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) ta bayyana cewa zazzabin lassa ta yi ajalin mutane 70 zuwa yanzu a Najeriya.

Hukumar ta sanar da haka a ratotan yaduwar cutar na mako ta biyar da ta gabatar ranar Talata.

Rahotan ya nuna cewa mutane 109 ne suka kamu da wannan cuta zuwa wannan mako.

Daga cikin mutane 109 dake dauke da cutar akwai ma’aikatan kiwon lafiya hudu daga jihohin Ondo, Delta da Kaduna.

Hukumar ta ce daga ranar 1 ga watan Janairu zuwa 9 ga watan Fabrairu hukumar ta gwada jinin mutane 1708 inda daga ciki ta samu mutane 472 da suka kamu da cutar sannan wasu 70 suka mutu daga kananan hukumomi 92 a jihohi 26.

NCDC ta ce har yanzu jihohin Edo, Ondo da Ebonyi ne suka fi fama da cutar a kasar nan.

Sannan mata musamman masu shekaru 21 zuwa 30 sun fi kamuwa da cutar fiye da maza.

Bisa ga wannan rahotan ma’aikatan kiwon lafiya sun yi korafin cewa gwamnati ta kasa taka rawan a zo a ganin wajen dakile yaduwar cutar a kasar nan.

Ma’aikatan kiwon lafiyan sun ce ana warkewa daga cutar amma duk shekara sai cutar ta bullo a kasar nan inda na wani shekaran yafi na wani shekaran cutar da mutane.

YADDA ZA A KIYAYE DAGA KAMUWA DA ZAZZABIN LASSA

1. Tsaftace Muhalli: A rika tsaftace muhalli a ko da yaushe. A kau da datti a kowani lokaci sannan a rika goggoge wuarare.

2. Zubar da Shara: Idan aka tara datti, kada arika barin su kusa da gida. A kai su can wajen da ake zubdawa a nesa ko kuma a rika konawa.

3. Killace Abinci: Yin haka zai taimaka wajen hana bera ko kwari shiga cikin abincin.

4. Dafa Nama: Kafin a dafa nama kamata a rika wanke shi da ruwan gishiri domin kashe duk wasu kwayoyin cuta dake jikin naman. A tabbatar naman ya dahu sosai kafin a ci.

5. Namun Daji: A nesanta kai daga yin mu’amula da namun daji musamman jinsin berayaye da birai.

6. Cin ‘ya’yan itatuwa: Kafin a ci ‘ya’yan itatuwa ko kuma ganye a rika wanke su sosai. Hakan na kau da datti a jikin su.

7. A daina barin dabbobin gida na shiga inda ake aje abinci: Kaji da wasu dabbobin da ake kiwon su a gida kan yi mu’amula da beraye a lokutta da yawa.

8. Toshe kafafen da suka bude: A tabbatar an toshe ramin da bera zai iya shiga cikin dakunan mu.

9. Tsafta: A yawaita wanke hannaye da ruwa da sabulu kafin da bayan an ci abinci sannan idan an kammala amfani da ban daki.

10. Ma’aikatan kiwon lafiya su tabbata sun nemi magani da zarar allurar da suka yi amfani da shi a jikin wanda ke dauke da cutar ya soke su.

11. Kona Daji: Kona daji na daga cikin hanyoyin dake koro beraye zuwa cikin gidajen mutane. A rika kiyayewa wajen kona dazukan dake kewaye da mu. Mai makon haka a rika feshin magani.

12. Wanke gawa a cikin Daki: Shima hakan na da illa matuka. Maimakon a rika wanke gawa a cikin gida a rika yin sa a waje ne ko kuma inda ya kamata.

Share.

game da Author