KISAN KIYASHIN AUNO: Buhari ya ziyarci Maiduguri

0

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ziyarci Maiduguri domin jajanta wa gwamnati da yan uwan mutanen da suka rasu a kisan kiyashin da Boko Haram sukayi ranar Lahadi.

Idan ba a manta ba a daren ranar Lahadi da misalin karfe 9:30 ne Boko Haram suka kashe mutane matafiya 30,banka wa motoci 18 wuta, sannan suka yi garkuwa da wasu a kauyen Auno.

Matafiyan sun yada Zango ne a Auno, kilomita 24 kusa da shingen tsaron sojoji kafin shiga Maiduguri.

Sojoji kan datse hanyar shiga Maiduguri tun 6 na yamma zuwa washegari, 6 na safe, babu shiga kuma ba fita.

A dalilin haka ne gwamnan Barno Babagana Zulum ya dora laifin kisan mutane 30 da kona motocin matafiya da Boko Haram suka yi a Auno, a kan abin da ya kira ma sakacin sojoji wajen kin maida hankali ga tsare Auno.

Zulum ya nuna bacin ran sa karara da fushi a safiyar Litinin, lokacin ya je garin Auno, ya gane wa idon sa irin mummunan kisan da Boko Haram suka yi wa matafiya a daren Lahadi.

Gwamnan Barno Babagana Zulum ya dora laifin kisan mutane 30 da kona gidaje da motocin matafiya da Boko Haram suka yi a Auno, a kan abin da ya kira ma sakacin sojoji wajen kin maida hankali ga tsare Auno.

Zulum ya nuna bacin ran sa karara da fushi a safiyar Litinin, lokacin ya je garin Auno, ya gane wa idon sa irin mummunan kisan da Boko Haram suka yi wa matafiya a Lahadi da dare.

Share.

game da Author