Jagoran kungiyar Jama’atul Ahlil Sunna liddawati wal jihad (Boko Haram), Abubakar Shekau ya yi kira ga mabiyan sa a fadin kasashen Afrika da Najeriya da su yi farautar Ministan Sadarwa Sheikh Pantami a ko ina a Najeriya.
Shekau yayi barazanar sai kungiyar sa sun ga bayan babban malamin muddun bai canja salon aikin sa ba.
Bayan Pantami, Shekau ya aika wa Buhari da Buratai sakonni na musamman a sabon bidiyon da ya fitar.
Haka kuma suma kafafen yada labarai, ya gargade su da su daina yi wa kungiyar katsalandan a ayyukants wajen kawo rahoton da ba haka ba kan kungiyar.
” A matsayina na shugaban kungiyar
Jamaatul Ahlil Sunna liddawati wal jihad (Boko Haram), ina yin kira ne ga dukkan ku munafukan addinin musulunci, wadanda suke ci da addini a boye.
” Mu fa bamu gaba da wani sai mun yi bincike mai zurfi mun gano sannan mun tabbatar cewa lallai dole mu yi maganin sa.
” Wannan bidiyo mun yi shi ne saboda mutum daya tal da ya ke ganin shi ya san komai. Ina so ya tabbatar ya adana wannan sako har zuwa ranar da mutuwa za ta zo masa. Daga yau zaka shiga cikin matsanancin damuwa da fitinan rayuwa, saboda ni Shekau na ce haka.
” Wannan sako ne zuwa ga Isa Ali Pantami. Kada ka dauka don ka na wa’azi da turanci sannan ana kiranka dakta shike nan wai ka san komai kenan. Bari in gaya maka baka san komai ba. Yanzu ka zama minista, kana ganin zaka iya cimma burinka yadda kake so ko? Kasa sani babu abinda ya hada musulunci da turanci.
” Kace kana so ka rufe layukan waya domin dankwafar da mu da kuma kuntata mana ko? Toh, ka sani sakonnin mu kamar mala’ikun Allah suke. Kai waye da za ka ce za ka iya tsaida ayyukan da muke yi ko kuma kawo mana cikas a aikin da muke yi wa Allah da addininsa. Wallahi ina tausayinka idan baka tuba.
” Na rantse da Allah kai ba komai bane. Ada ba mu da matsala da kai amma yanzu ka zama bawan kafirai. Ka yi maza-maza ka tuba, ka zama musulmi nagari.
” Idan baka tuba ba toh, lallai kuwa mutuwa na gab da iske ka. Ina kira ga duk mabiyan mu dake Afrika da Najeriya su yi abinda ya kamata.
“Muna so ka sani cewa abinda muka yi wa sheikh Jaafar ba wani abu bane, wato soman tabi ne.
” Duk inda kuka hango ko kuka ci karo da Ali Pantami, kada ku barshi ya rayu. Pantami, baka ishe mu kallo ba ma domin kai ba komai bane.
” Ko Ja’afar ya nemi ya shiga mana hanci amma mun yi maganin sa ballantana kai da kwaro ne a musulunci. Ina so ka sani daga yau zaman lafiya ya kare maka Pantami, saboda ka fusatar da Allah.
Sakon Shekau ga Shugaba Buhari
” Kai kuma Buhari, ba ka kusa cika shekaru 80 ba? Amma kana ta galantoyi sai yawo kake ta yi, ga shi yanzu mutanen da kake tunkaho da sun fara yi maka Ihu, ina so ka sani cewa yanzu fa mala’ikun mutuwa kawai kake jira.
” Kawai da ga wasu sun gaya maka cewa sun kashe wasu daga cikin kwamandojinmu shi ke nan sai ka dyi zaton ka yi nasara. Yanzu Shekau kake hari kake so ka kashe ko? Ina so ka sani cewa kai Buhari ka shiga uku, kana cikin tashin hankali babba kuwa, ina so ka san haka.
Sannan kuma kai Buratai, mun ga kamar ka gaji ne ko, ka saurari ranar ka kaima domin tananan zuwa.
Daga nan kuma sai Shekau ya yi gargadi da kakkausar murya ga gidajen jaridu kamar su BBC, Jamus, Faransa da sauran jaridun Najeriya da su shiga taitayinsu, su dai na fadi ko rubuta abinda ba haka ba game da ayyukan Boko Haram din.”