CORONAVIRUS: Wani ya kamu da cutar a Kasar Masar

0

A karon farko an tabbatar da bayyanar cutar CoronaVirus a nahiyar Afrika inda aka samu wani ya kamu da ita a kasar Masar, wato Egypt.

Ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Masar, ta tabbatar a haka inda tace wani matafiyi ne da ya shigo kasar ya kamu da ita.

Ma’aikatar ta bayyana cewa tuni har an killace wannan matafiya a wani asibiti sannan an ci gaba da bincike domin kada cutar ta yadu.

Ma’aikatar ta ce tunda aka samu tabbacin kamuwar wannan cuta ta gaggauta sanar da Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya domin a dauki matakin gaggawa.

Wannan shine karo na farko da za a tabbatar da bayyanan cutar a nahiyar Afrika.

A yankin gabas ta tsakiya kuma, yawan wadanda suka kamu sun kai akalla mutum 9 kenan baya ga mutane 8 da aka tabbatar sun kamu a kasar UAE sai kuma kasar Masar yanzu.

Kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta bayyana cewa rashin gaggauta daukan mataki wajen dakile yaduwar cutar coronavirus na iya tada zaune tsaye a fadin duniya.

Shugaban kungiyar Tedros Ghebreyesus ya sanar da haka ranar Litini yana mai cewa hankalin kungiyar ya tashi matuka ganin cewa mutanen da basu taba zuwa kasar Chana ba na kamuwa da cutar.

A ranar Lahadi hukumar kiwon lafiya dake kasar Britaniya sun gano cutar a jikin wasu mutane biyar da suka dawo daga kasar Faransa.

Daga nan kuma sai wani mutum daya ya kamu da cutar shima bayan ya dawo daga kasar Singapore.

WHO ta ce dole fa hankalinta ya tashi yanzu kam ganin cewa cutar na ci gaba da yaduwa kuma har yanzu ba a samu maganin ta ba ko kuma maganin rigakafin ta.

Ghebreyesus ya yi kira ga kasashen duniya da su karfafa makatan hana yaduwar cutar a kasashen su cikin gaggawa.

Ya kuma ce kungiyar za ta ci gaba da tallafa wa kasashen da basu da karfin dakile cutar ta hanyar bude wuraren yin gwajin cutar a kasashen su.

WHO ta aika da na’urorin gwajin cutar da abin toshi baki da hanci zuwa kasashen Kamaru, Côte d’ivoire, Egypt, Ethiopia, Gabon, Ghana, Kenya, Morocco, Nigeria, Tunisia, Uganda da dai wasu kasashe domin tallafa musu wajen inganta matakan hana yaduwar cutar.

Wuraren yin gwajin cutar da ake da su a duniya suna kai 168.

Bayan haka kungiyar ta aika da wasu kwararrun likitoci da za su hada hannu da likitocin kasar Chana domin gano hanyoyin da suka fi dacewa wajen dakile yaduwar cutar.

Sannan kungiyar ta kuma kawo kayan gwaji guda 150,000 domin inganta wuraren yin gwajin cutar guda 80 dake Berlin, Kasar Jamus.

Kwayoyin cutar CoronaVirus na daga cikin kwayoyin cutar dake sa a kamu da mura wanda idan yayi tsanani akan yi fama da matsalar cutar dake hana numfashi yadda ya kamata da ake kira (Middle East Respiratory Syndrome (MERS-CoV), da kuma cutar tsanannin mura da kan toshe makogoro.

Akan kama cutar ne a dalilin cudanya da dabbobi domin sune ke dauke da ita. Sakamakon bincike da aka yi game da cutar ya nuna cewa akan kamu da cutar ne ta hanyar yin muamula da dabbobi na gida da na daji.

Alamun kamuwa da cutar sun hada da matsala a kafofin wucewar iska a makogoro wato numfashi, yawan zazzabi, tsananin tari, da ciwo a makogoro.

Haka kuma idan abin yayi tsanani, ya kan kai ga shakar iska ma ya gagara, sannan a samu matsalar sanyin hakarkari wato ‘Nimoniya’, kuma idan har ya yi tsanani matuka kodar mutum kan daina aiki kwata-kwata.

WHO ta ce mutane 40,235 ne ke dauke da cutar sannan wasu 909 sun rasu a dalilin kamuwa da cutar a kasar Chana.

Sannan bayan kasar Chana cutar ta bullo a kasashen duniya 24 inda akalla mutane sama 319 suka kamu da cutar da ya mutu.

Share.

game da Author