WASA YA BACI: An kori Manchester City daga buga gasar Champions League

0

Hukumar Shirya Gasar Kwallon Kafa ta Turai (UEFA), ta haramta wa kungiyar Manchester City shiga gasar wasannin Champions League tsawon shekaru biyu. Kuma an haramta mata shiga Europa tsawon wadannan shakaru.

Sannan kuma an dankara mata tara ta dala fam milyan 30. Wadannan adadin kudaden sun kai naira bilyan 14.2 na kudin Najeriya.

An dankara mata wannan hukunci mai tsauri ne bayan da Kwamitin Bincike na UEFA ya kama kulob din da dirka karya bayyana ribar da ta samu a tallace-tallace daga kamfanoni a kakar wasannin 2012 da kuma 2016.

An kafa kwamitin binciken ne bayan da wata mujallar kasar Jamus mai suna Der Spiegel ta fallasa yadda wani magulmaci ya ba su bayanan takardun shaidar laifin da Manchester ta tabka.

Der Spiegel ta buga labarin a cikin watan Nuwamba, 2018.

Sai dai kuma za ta ci gaba da wannan gasar da ake kai, wadda a zagaye na biyu a moko mai zuwa za ta kara da Real Madrid ta Spain.

Amma kuma a shekarar 2020/2021 da 2021/2022, ko da ta zo ta daya a gasar Premier, ba ta za buga Champions League ba.

Idan ba a manta ba, an taba maida Juventus ta Italliya rukuni na uku daga rukuni mafi daraja a kasar, wato Seria A, bayan samun kulob din da hada baki wajen yin nasara a wasu wasanni ta hanyar zamba da harkallar toshiyar baki.

Share.

game da Author