A kokarin da Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ke yi domin ganin lallai sai ta tara harajin naira tiriliyan 8.5 a cikin shekarar 2020, Hukumar Tattara Haraji ta Kasa ta yi manyan canje-canje ga Daraktoci 50.
Baya ga wadannan Daraktoci su 50, PREMIUM TIMES kuma ta tabbatar da cewa sauyin ya shafi wasu manyan jami’an hukumar ta FIRS su 100.
Sai dai kuma yayin da daga likkafar wasu zuwa gaba, domin a zaburar da su wajen maida himma ga tattara kudaden haraji, an kuma yi wa da dama canjin wurin aiki daga wasu jihohi zuwa babbar hedikwatar FIRS da ke Abuja.
Idan ba a manta ba, Fadar Shugaban Kasa ta yi korafi a cikin 2019 ga tsohon shugaban Hukumar Tattara Haraji, Babatunde Fowler, dangane da kasa tattara kudade kamar adadin da Gwamnatin Goodluck Jonathan ta tattara cikin 2012 da 2013.
Ana ganin bisa wannan dalili ne aka ki sake nada shi zango na biyu, bayan da wa’adin zangon sa na farko ya kare a cikin Nuwamba, 2019.
An maye gurbin sa da Muhammad Namu, wanda tuni ya kama aiki, inda farkon aikin sa shi ma ya gwasale FIRS a karkashin Fowler, ya ce ba ta tattara makudan kudaden da ya kamata ta tattara ba, duk kuwa da karin ma’aikatan da aka yi fiye da lokacin Jonathan.
Namu ya kama ragamar shugabancin FIRS ne da kudirin lallai sai ya tattara akalla naira tiriliyan 8.5 a cikin wannan shekara ta 2020.
Majiya ta ce ya yi wannan canje-canje ne domin ya gurguso da wasu da ya amince da su, wadanda ya ke ganin za su iya jajircewa su taimaka masa ganin cewa ko ana ha-maza-ha-mata FIRS ta tattara harajin naira tiriliyan 8.5 cikin 2020.
Tuni dai Buhari ya sa wa Dokar Harajin Jiki-magayi (VAT) hannu, inda a yanzu ya tashi daga kashi 5% ya koma 7.5. Kuma daga ranar 1 Ga Fabrairu mai zuwa za a fara cirar kudaden.