Uwargidan gwamnan jihar Kebbi Zainab Bagudu ta yi kira ga gwamnati da a yi wani doka da zai tilasta mutane yin gwajin cutar daji da zarar mutum ya kai wasu shekaru a raye.
Zainab wacce ita ce mai mallakin gidauniyar ‘MedicAid Cancer Foundation’ ta bayyana cewa yin haka zai taimaka matuka wajen kawar da matsalolin da gwamnatocin tarayya da na jihohi ke fama da su a wajen kau da cutar.
Ta ce sai dai hakan zai yiwu ne idan gwamnati ta ware isassun kudade domin gina ingantattun asibitoci domin gwaji da kula da masu fama da cutar a kasar nan.
Idan ba a manta ba a watan Oktobar 2019 uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta yi kira da a rika wayar da kan mutane game da wannan cuta cewa yin haka zai taimaka wajen dakile yaduwar cutar.
Ta ce kamata ya yi Najeriya ta yi koyi sannan da kirkiro hanyoyi domin kawar da wannan cuta da wasu kasashen Afrika suka yi.
Discussion about this post