Atiku ya goyi bayan kafa Dakarun Amotekun

0

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya goyi bayan kafa Dakarun Tsaron Jihohin Kudu maso Yamma, da aka fi sani da suna Amotekun.

Gwamnonin Jihohin Lagos, Ekiti, Oyo, Osun, Ogun da Ondo ne suka kafa dakarun a farkon Janairun 2020.

Sai dai kuma Gwamnatin Tarayya, ta hannun Ministan Shari’a, Abubakar Malami ta haramta Amotekun. Tun bayan haramta kafa su ne ake ta ka-ce-na-ce tsakanin masu goyon bayan Amotekun da wadanda ba su goyon baya.

Atiku ya ce gagarimar matsalar tsaron da kusan kowace jiha a kasar nan ke fuskanta, ta sanya akwai matukar bukatar kafa kungiyoyin tsaro a jiha, yanki da cikin al’umma.

Atiku ya ce daga shekaru goma da suka gabata zuwa yau, aikin gudanar da tsaro ya ci karfin jami’an ‘yan sanda matuka, saboda famar da suke yi wajen kokarin dakile rigingimu da hare-hare.

Ya ce hakkin gwamnati ne ta tabbatar da ta kare rayuka, lafiya da dukiyoyin ‘yan kasa. Amma saboda mawuyacin halin matsalar tsaro da kasar nan ta afka, wajibi ne a kafa wasu kungiyoyin tsaro da za su iya taimaka wa jami’an ‘yan sanda, musamman a wuraren da babu ‘yan sanda cikin lungunan kasar nan.

Atiku, wanda ya yi takarar shugaban kasa a karkashin PDP a zaben 2019, ya ce abin takaici ne da wasu ke kokarin siyasantar da Amotekun. Ya ce bai kamata ba, kuma ma ganganci ne a rika tsarma siyasa a cikin batun tsaro.

A nasa tunanin, ya ce masu kushe kungiyoyin tsaro irin su Amotekun, su ne ma barazana ga kasa, ba kungiyar Amotekun ba.

Wasu da dama na ganin cewa bai yiwuwa Jihohin kudu su zauna su na gani hare-hare ya yi tsanani a Arewa, su kuma su zauna su zura ido. Ko na komai, a ganin su, ai abin da ya ci garin Doma, ba zai bar garin Awai ba.

Share.

game da Author