Lokacin fara batun shugabancin 2023 bai yi ba tukunna –Tinubu

0

Babban jagoran APC Bola Tinubu, ya ki yarda ‘yan jarida su jefa shi cikin rudanin siyasar shuagabanci bayan wa’adin 2023 da kuma batun tsarin karba-karba, wadanda ya ce lokacin tattauna su bai yi ba tukunna.

Tinubu ya bayyana haka ne a jiya Talata ga manema labarai bayan ya fito daga Fadar Shugaban Kasa, inda ya yi ganawar sirri da Shugaba Muhammadu Buhari.

“Duk wanda ka ga ya fara maganar shugabanci a 2023 ko batun tsarin karba-karba tun yanzu, to gigitacce ne, kuma bai maida hankali kan kokarin gina kasar nan da tattabar da ci gaban ta da ake kan yi a yanzu ba.” Haka Tinubu ya shaida wa manema labarai na Fadar Shugaban Kasa.
.
Daga nan kuma sai Tinubu, wanda ake kallon cewa ya na son tsayawa takarar shugabancin kasar nan a zaben 2023 ya yi magana a kan kara jaddada kammala shiga zabe da Buhari ya ce ya yi tun daga zaben 2019.

Ya ce shi dai ya je Fadar Villa ce domin ya yi wa Shugaba Buhari murnar shiga sabuwar shekara kuma ya kara yi masa fatan alheri
Tinubu ya ce sakon Buhari na karshen shekara ya shiga kunnuwan jama’a da dama, kuma ya tabo bututuwa masu muhimmanci, musamman batun tsaro da sauran su.

Da aka yi masa magana a kan sake tsayawa takarar da ake surutai wai Buhari na kokarin yi, sai Tinubu ya ce, “ai duk wani mai hankali ya san Shugaba Buhari mutum ne mai bin tsarin da dokar kasar nan ta shimfida, kuma babu yadda za a yi a ce zai yi wa dokar Najeriya karan-tsaye.

“Don haka idan Buhari ya kammala zangon sa na biyu, tafiya zai yi ya huta, ko an yi masa tayi ma ba zai karba ba, saboda ya san ya kammala abin da doka ta shar’anta masa.”

Batun karba-karba kuwa, sai Tinubu ya ce a yanzu dai ba a dade da fara mulki zango na biyu ba, kuma yanzu shugaban kasa da gwamnatin sa sun maida hankali ne a kan kasafin kudi da za a fara aikin gina kasar nan da shi.

“Don haka lokacin fara batun karbar mulki a 2023 bai yi ba tukunna.”

Share.

game da Author