Babban Lauya Femi Falana ya bayyana cewa hauragiyar surutai babu kan-gado da Ministan Shari’a Abubakar Malami ke yi, a kan dalilan sakin Sambo Dasuki da Omoyele Sowore, su na tozarta gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.
Baya ga tozarta gwamnatin, Falana ya kara da cewa wadannan surutai na zubar da kimar fannin shari’a a Najeriya, ta yadda shari’a a kasar nan ta zama abin dariya, abin gwasalewa da yi wa habaici.
Duk da cewa kotuna da dama ne suka bayar da umarnin a saki mutanen biyu, shi kuma Ministan Shari’a Malami duk inda ya zauna, ya na cewa gwamnati ta sake su ne saboda tausayi.
SSS sun tsare Dasuki tsawon shekaru hudu, yayin da suka tsare Sowore tsawon watanni hudu, duk kuwa da cewa sunn cika sharuddan belin da kotu ta gindaya musu.
Sai dai kuma gwamnati ta sake su cikin watan Disamba, bayan da kungiyoyin rajin kare hakkin jama’a da na kasa da kasa suka matsa wa Najeriya lamba, a kan kauce wa turbar dimokradiyya da gwamnatin Buhari ke yi.
A bayanin da ya fitar kwanan nan, Falana ya kara jaddada matsayar sa cewa gwamnati ba ta da wani dallili mai karfi ko raunana da za ta iya rufe ido ta dogara da shi har ta ci gaba da tsare su Dasuki da Sowore, tunda har kotu ta ce a sake su.
Ya ce abin kunya ne da kuma zubar da kimar gwamnati da martabar shari’a har Minista Malami ya rika fitowa a kafafen yada labarai ya na cewa jin kai da tausayi ne suka sa gwamnati ta saki Dasuki da Sowore a ranar 24 Ga Disamaba, 2019.
Falana ya kalubalanci Malami cewa ba shi da iko domin doka ba ta ba shi iznin sakin wanda ke fuskantar shari’a domin jinkai ko tausayin sa ba.
Kwan-gaba-kwan-bayan Minista Malami
Babban Lauya Falana ya ce idan akwai wurin da kotu ta ba shi ikon sakin wanda ake tuhuma don tausayawa ko jinkai, to kawo wurin, domin dokar kasar nan ta 175 dai ba ta bada wannan iznin ba.
Ya ce don me Malami zai rika fitowa ya na surutai barkatai wai saboda tausayi, alhali kuma kotu ce ba sau daya ba, ba kuma sau biyu ba ta ce a sake su.
“Ya ka na Ministan Shari’a za ka ki bin umarnin kotu ka saki mutum, sannan bayan an tirsasaka ka sake shi, kuma ka dawo ka na cewa wai saboda tausayi da jinkai.”
Falana ya kuma cika da mamakin yadda Malami a baya ya rika cia-bakin cewa, “gwamnatin tarayya ba za ta sake su ba har sai an ga yadda karar da aka daukaka ta kaya.”
Lauyan ya ce duk maganganun da Malami ke yi hauragiya ce kawai, babu gaskiya ko guda daya tal a ciki.
Daga nan sai ya yi nuni da cewa karar da ma ya ce an daukaka duk walle-walle ce, domin ofishin DSS ba su bi kadin daukaka kara ba, sai suka rika tsayawa wai tantance wadanda za su karbi beli, alhali kuma kotu ce mai bada beli, ta rigaya ta ba su, kuma ta amince da su.
Daga nan kuma sai Falana ya tunatar da cewa sau shida alkalan Babban Kotun Tarayya daban-daban su na bada belin Dasuki, sai kuma Babbar Kotu ta bada belin sa sau daya.
Falana ya ce babu ko sau daya inda a wadannan wurare gwamnatin tarayya ta daukaka kara.
“Farkon belin ma ai lauyan gwamnati Abubakar Diri bai yi jayayya a kotu ba. To don me kuma Malami zai rika surutai da bulkarar daukaka kara, alhali lauyan gwamnati bai yi jayayya da belin da kotu ta bayar ba?”
“Ai Dasuki ne ya gaji da yadda gwamnatin tarayya ke wa shari’ar sa asarkala, sai ya kai kara Kotun ECOWAS, inda ita ma ta ce a sake shi, sannan kuma ta ci gwamnati tarar biyan sa diyya har naira milyan 15 a ranar Ga Oktoba, 2019.”
A kan tuhumar da ake wa Dasuki da zargin karkatar da dala bilyan 2.1 na makamai kuwa, Kotun ECOWAS cewa ta yi:
“Duk wanda ake zargi ya yi irin wannan laifin kuma har kotu ta tabbatar da ya aikata, to tilas ne a hukunta shi. Amma fa duk bincike da gurfanarwa da tuhuma da kuma yanke masa hukunci, to a tabbatar cewa gwamnati ta gudanar da su a bisa tsarin da dokar kasa ta gindaya da kuma bin umarninn kotu.”
An saki Dasuki da Sowore a ranar 24 Ga Disamba, 2019, aka ce su rika kai kan su kotu a duk ranar da shari’ar su ta taso.