Shugaba Muhammadu Buhari ya bada umarnin a gaggauta soke dakatarwar Shugabar Hukumar Inganta Wutar Lantarki a Karkara (REA), Damilola Ogunbiyi.
Wannan umarni da Buhari ya bayar ya soke dakatarwar da Ministan Lantarki Sale Mamman ya yi wa Ogunbiyi.
Mamman ya dakatar da Ogunbiyi cikin watan Disamba, bisa abin da sanarwar dakatarwar ta bayyana da cewa an sabu baddalallen lissafi kuma ba ta tabuka abin kirki a kan aikin ta.
Sanarwar ta kara da cewa dakatar da ita zai kawo saukin gudanar da bincike domin gano inda matsalolin hukumar suka cukurkude.
PREMIUM TIMES ta kuma kawo rahoton yadda aka nada karamin ma’aikatacin gwamnati kan mukamin da Ogunbiyi ta ke a kai.
Binciken da PREMIUM TIMES ta gudanar ta gano cewa Ahmad karamin ma’aikaci ne a Hukumar ICRC kafin a nada shi.
Sannan kuma ita kan ta ICRC din an kafa ta ne a cikin 2018. Kuma Ahmad da ne ga marigayi Salihijo Mohammed Ahmad, tsohon shugaban kamfanin Afri Consortium, wanda ya yi aikin kwangilolin tuntuba tare da Buhari a zamanin PTF.
Sannan kuma an samu hayaniya a Hukumar Lantarki ta BET PLC, bayan dakatar da shugaban kamfanin, Marilyn Amobi.
PREMIUM TIMES ta kuma buga labarin yadda SSS suka damke wasu ma’aikatan hukumar su tara aka tsare su, bayan kama Marilyn.
Sai dai kuma wadda aka dakatar din tuni har ta kama aiki a Majalisar Dinkin Duniya.