A ranar Litini ne majalisar dokokin jihar Kano ta amince wa gwamnan jihar Abdullahi Ganduje ya ciyo bashin Naira biliyan 15 domin inganta fannin ilimin jihar.
Majalisar ta yi haka ne bayan kwamitin harkokin kananan hukumomi na majalisar ta gabatar da sakamakon binciken da ta yi kan wannan kudiri.
Bisa ga sakamakon binciken da shugaban kwamitin kuma mataimakin shugaban masu rinjaye na majalisar, Kabiru Hassan–Dashi ya gabatar ya nuna cewa ciyo wannan bashi zai taimaka wajen inganta fannin ilimin jihar musamman a bagaren gina sabbi da gyara tsoffin ajujuwa domin rage yawan cinkoson dalibai a makarantun gwamnati dake jihar.
Sannan za a dinka wa dalibai kayan makaranta tare da ciyar da su abinci kyauta a makarantun gwamnati.
A dalilin haka ne majalisar wanda kakakin majaisar Abdulazeez Garba-Gafasa ya jagoranta ta amince wa gwamnatin jihar ta ciyo bashin.
Idan ba a manta ba far wannan mako ne gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya nemi majalisar dokokin jihar da ta amince wa gwamnati ta ciyo bashin Naira biliyan 15 domin inganta fannin ilimi a jihar.
Kakakin majalisar Abdulazeez Garba-Gafasa ya karanta wasikar neman bashin da gwamna Ganduje ya aiki a ranar Litini a zauren majalisar.
Garba-Gafasa ya ce Ganduje zai yi amfani da wadannan kudade ne wajen inganta ilimin boko kyauta a kananan hukumomi 44 a jihar.
Ya ce gwamnatin za ta biya bashin wadannan kudade ne daga cikin kason kudaden da gwamnati ke bata a duk wata tare da riban kasha 15.
Baya ga haka Garba-Gafsa ya gabatar da wasikar ga kwamitin harkokin kananan hukumomi na majalisar domin duba wannan himma na gwamnatin jihar.
Majalisar ta bai wa kwamitin kwanaki biyu ta mika rahoton ta.