Sakamakon binciken da jami’ar ‘John Hopkins’ ta yi ya nuna cewa nan da shekaru 10 masu zuwa Najeriya za ta iya rasa yara ‘yan kasa da shekaru biyar akalla miliyan biyu a dalilin kamuwa da cutar sanyi ‘Nimoniya’.
Jami’ar ta gabatar da wannan sakamako ne a taron bita da ta yi da kungiyoyin bada tallafi na duniya da suka hada da IsGlobal, Save the Children, UNICEF, Every Breath Counts, gidauniyar ‘La Caixa’, gidauniyar Bill da Melinda Gates, USAID; Unitaid da Gavi, the Vaccine Alliance a kasar Barcelona ranar Laraba.
Sakamakon binciken ya nuna cewa inganta kiwon lafiyar yara kanana musamman a bangaren allurar rigakafi, shayar da jarirai nono, ciyar da yara abincin da zai gina musu garkuwan jiki na daga cikin hanyoyin da zai taimaka wajen ceto rayukan akalla yara 809,000 a kasar nan.
Cutar sanyi dake kama hakarkari ‘Pneumonia’ cuta ce na sanyi dake kama hakarkarin mutum a dalilin shakan gurbataccen iska da kuma yawan amfani da abubuwan sanyi.
Bincike ya nuna cewa kwayoyin cuta na ‘Virus, Bacteria da Fungi’ ne ke haddasa wannan cuta.
Cutar na daya daga cikin cututtuka biyar dake kisan yara kanana ‘yan kasa da shekaru biyar a duniya.
Sannan an gano cewa a duk shekara cutar kan yi sanadiyyar rayukan yara kanana akalla kashi 19 bisa 100 a Najeriya.
Alamun wannan ciwo sun hada da zazzabi, rashin iya numfashisosai, ciwon hakarkari, rashin iya cin abinci, suma da sauran su.
Wakilai sun yi kira ga masu ruwa da tsaki a harkar kiwon lafiyar kasar nan da su maida hankali wajen samar da dukkan kariyar da ake nema domin kauce wa wannan matsala dake tunkarowa.
Hanyoyin gujewa kamuwa da Ciwon Sanyin Hakarkari ‘NIMONIYA’
1. Tsaftace muhalli
2. Gujewa shakar gurbataccen iska musamman hayakin risho, itace, bola da sauran su.
3. A daina zama inda ake yawan cinkoso.
4. A daina shaka da zukar taba sigari.
5. Cin abincin dake kara karfin garkuwan jiki musamman ga yara kanana.
6. Yin allurar rigakafin tarin lala, bakon dauro da ciwon hakarkari.
7. Za a iya amfanin da maganin kara karfin garkuwan jiki ‘Antibiotics’ domin kawar da cutar.
8. Iyaye za su iya shayar da ‘ya’yan su ruwan nonon na tsawon shekara daya domin nono na dauke da sinadarorin dake kare yara daga kamuwa da cutar.
9. Iyaye sun kare ‘ya’yan su daga kamuwa da cutar kanjamau.