Hukumar kula da dalibai masu yi wa kasa hidima (NYSC) ta sanar cewa za a fara biyan alawus din daliban da sabuwar tsarin mafi kankantar albashi.
Shugaban hukumar Shuaibu Ibrahim ya sanar da haka a sansanin horas da masu yi wa kasa hidima a jihar Bauchi.
Ibrahim ya ce daga yanzu gwamnati za ta rika biyan masu yi wa kasa hidima Naira 33,000 a matsayin alawus din da zarar gwamnati ta kammala wannan tsari.
Ya kuma yi kira ga masu yi wa kasa hidima da su guji yin tafiyar dare da kuma nisanta kansu daga amfani da yanar gizo ta hanyoyin da bai kamata ba.
Idan ba a manta ba a ranar 18 ga watan Afrilun 2019 ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya saka hannu a takardan biyan ma’aikata da sabuwan tsarin mafi kankantan albashi.