Bude kan iyakoki ba yanzu ba tukunna – Inji Buhari

0

Shugaba Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa har yanzu bai bayyana ranar da za a sake bude kan iyakokin Najeriya ba tukunna.

Ya ce kan iyakokin Najeriya za su ci gaba da kasancewa a rufe, har zuwa lokacin da aka ga bukatar sake bude su din ta taso.

Sai dai kuma Shugaba Buhari ya ce ba za a yi saurin bude kan iyakokin ba, sai al’amurra su fara gyaruwa sosai tukunna.

An dai rufe kan iyakokin Najeriya tun cikin watan Agusta, kuma a cikin Oktoba ne Shugaban Hukumar Kwastan, Hamid Ali ya bayyana cewa, “an haramta shigo da kowane irin kaya da kuma fitar da kowane irin kaya, har zuwa lokacin da al’amurran suka inganta tukunna.”

Wannan ne karo na farko da aka bayyana rufe kan iyakokin ruf.

Ya ce sake bude kan iyaka “ya dogara ne a kan irin kwakkwarann hadin kai da kasashen da Najeriya suka bayar wajen bin ka’ida da kuma kiyaye sharuddan cinikayyar kasashen da ke makwauta ko suka hada kan iyaka da juna.”

Saboda wannan rufe kan iyakoki ya shafi Jamhuriyar Nijar da Benin, sai aka zauna aka rattaba sa hannun ka’idoji da sharuddan da Najeriya ta nemi a cika kafin ta sake bude kan iyakokin.

PREMIUM TIMES ta buga wadannan ka’idoji a farkon wannan wata, ta ce su ne ta ke so kasashen ta cika.
Ka’idojin dai su na cikin kundin ka’idojin harkar cinikayyar kasashen Afrika.

Ko Akwai Alfanun Rufe Kan Iyaka?

Shugaban Kasa ya bayyana cewa an rage shan fetur kusan kashi 30 bisa 100 a cikin Najeriya. Wannan kuwa an fassara dalilin hakan cewa alama ce da ke nuna kusan kashi 30 bisa 100 na fetur din Najeriya, duk fitar da shi ake yi a kasashen waje kenan

Kakakin Yada Labarai na Fadar Shugaban Kasa, Garba Shehu, ya ce Buhari ya yi wannan jawabi a garin su Daura, lokacin da ya karbi bakuncin Kungiyar Dattawan Jihar Katsina.

Ya karbe su ne a Daura, garin sa na haihuwa cikin Jihar Katsina.

Buhari ya yi hutun karshen mako ne a Daura, inda a ranar Litinin kuma ya kaddamar da fara aikin gina Jami’ar Fasahar Sufuri a Daura.

A jiya Litinin, Buhari ya ce an rufe kan iyakoki ne domin a magance sumogal din kayayyaki zuwa cikin Najeriya, musamman shinkafa, kuma hakan a cewar sa, ya samar wa Najeriya makudan kudaden da a baya kwasar su ake yi ana fita ana sayo shinkafa dga wasu kasashe.

Buhari ya jinjina wa Shugaban Jamhuriyar Nijar dangane da hadin kan da ya ke bai wa Najeriya, musamman korar wasu jami’an kasar da kuma haramta jibge kayan sumogal cikin kasar Nijar, wadanda ake tarawa a can, kafin a rika shigo da su Najeriya ta barauniyar hanya.

Share.

game da Author