Matawalle ya saya wa ‘yan majalisar jihar sabbin motoci na kasaita

0

Gwamnatin jihar Zamfara ta raba wa ‘yan majalisar dokoki na jihar motocin kasaita har 24.

Maitaimaka wa gwamna Bello Matawalle, kan harkokin yada labarai Yusuf Idris ya sanar da haka da yake tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a garin Gusau ranar Talata.

Idris yace gwamna Matawalle da kansa ne ya mika wadannan motoci kirar ‘Toyota Camry 2018 V6’ wa ‘yan majalisar.

Sai dai Idris bai fadi yawan kudin da gwamnati ta kashe ba wajen siyo wadannan manyan motoci.

“Ba ya ga ‘yan majalisun kaf da aka raba wa wadannan motoci, a kwanakin baya gwamnati ta raba wa shugabannin majalisar motoci kirar ‘Jeep’.

Idris ya kara da cewa gwamnatin Matawalle zara yi kokarin ganin ba a samu wata baraka ba a tsakanin gwamnati da ‘ya ‘yan jam’iyyar.

Jami’in hulda da jama’a na majalisar dokokin jihar Mustafa Jafaru- Kaura ya musanta rade-radin da ake ta yadawa wai gwamnati ta raba wa ‘yan majalisar motocin a matsayin bashi ne.

Kaura yace baya ga Toyota ‘Saloon’ da aka rabawa ‘yan majalisan, ya shugabannin majalisar an basu manyan motoci kirar ‘Jeep’.

Wani ma’aikacin majalisar ya tsokata wa PREMIUM TIMES cewa gwamnati ta kashe sama da naira Miliyan 400 wajen siyan wadannan motoci.

Ya ce gwamnati ta kashe akalla Naira miliyan 17.5 wajen siyan wadannan motoci ga kowane dan majalisar jihar.

Share.

game da Author