‘Yan Najeriya sun fi kasashen Afrika ta Yamma da dama samun wutar lantarki –Jami’ai

0

An bayyana cewa kasashe biyar na Afrika ta Yamma da suka hada da Cape Verde, Ghana, Senegal, Najeriya da Cote D’ivoire su ne kan jerin kasashen da ke gaba wajen shan garbasar hasken lantarki a Afrika ta Yamma.

Wadanda kuma suka fi fama da matsalar wuta, sun hada da Gambiya, Saliyo da kuma Togo, kamar yadda Babban Daraktan Hukumar Tattalin Makamashi na Afrika ta Yamma, ECREEE, mai suna Mahama Kappiah ya bayyana a wani taro da aka gudanar ranar Litinin a Abuja.

Kappiah ya ce kashi 42 kadai bisa 100 ne na daukacin al’ummar Afrika ta Yamma ke samun wutar lantarki, yayin da kashi 8 kacal bisa 100 ne na mazauna karkarar kasashen Afrika ke iya samun hasken lantarki.

Ya ce mutanen da ba su iya samun hasken lantarki a Afrika ya Yamma sun kai milyan 175. Daga nan sai ya yi kiran cewa ya kamata a kara tashi haikan tsaye domin ganin an inganta rayuwar al’ummar karkara da hasken lantarki.

Ya bada alwashin cewa mutane milyan 1.7 ne za su ci moriyar shirin samar da makamashin lantarki na ROGEP.

Shirin inji shi zai ci kimanin dal milyan 223, kuma zai inganta hasken lantarki a Afrika ta Yamma da yankin Sahel ta hanyar amfani da karfin hasken rana da solar.

Shirin kuma kamar yadda Kappiah ya jaddada, zai amfani kamfanonin solar da masu harkokin ta daga kasashen ECOWAS da Mauritaniya, Kamaru da kuma Chadi.

“Inda shirin ROGEP a karkashin aikin samar da hasken lantarki na ECREEE zai maida hankali kuma bayan kammala wannan, shi ne maida hankali ga aikin a Ghana, Guinea, Najeriya da Sanagal, saboda daga wadannan kasashe ne aka samun yawan fitar masu gudun hijira.

Share.

game da Author