Bayelsa jihar ce mai abin mamaki. Ta fi sauran jihohin kasar nan kankantar yawan jama’a, domin kananan hukumomi 8 ne kadai a jihar. Amma dimbin arzikin man fetur din da ke shimfide a jihar, ya sa Bayelsa na sahun gaban jihohin Kudu maso Kudu masu arzikin fetur din da ke ciyar da Najeriya.
Wannan dalili ne ya sa duk wani hamshakin dan siyasa na Bayelsa ke kokarin ganin cewa jihar sa ce ta lashe zaben gwamna. Domin me, ko ba komai dai kudaden da gwamnatin tarayya ke dankara wa jihar duk karshen wata, sun zarce yawan na wasu jihohin Arewa da yawa, ko da kuwa an hada da Kano.
INEC ta bayyana cewa mutane 889,308 ne suka karbi katin zaben su, daga cikin 923,182 wadanda suka yi rajista.
Bayelsa na da mazabu 1,804 cibiyoyin rajista kuma 105.
Duk wani dan takara a Jihar Bayelsa zai so ya ci kuri’u masu tarin yawa a Karamar Hukumar Yenagoa, saboda ita ce babban birnin jihar, kuma ta fi sauran kananan hukumomi yawan masu jefa kuri’u.
Zaben jihar Bayelsa zai zama iya-ruwa-fidda-kai, domin kowa zai nemi yin nasara a kananan hukumomin takwas, wadanda kowacen su a a tsakiyar ruwa suke tsullum.
Sauran kananan hukumomin bakwai sun hada da Brass, Eketomor, Kolokuma/Opokuma, Nembe, Ogbia, Sagbama da Ijaw ta Kudu.
Karamar Hukumar Ijaw ta Kudu nan ne aka fi yawan tashin hankula, domin a cikin wannan makon an kashe mutum shida a rikicin siyasa, wanda aka zargi magoya bayan APC da yin aika-aikar.
Zaben gwamna a Bayelsa zaben gwada gwanittar wanda ya fi iya ruwa ne, tsakanin gwamna mai ci yanzu, Dickson, wanda ke kammala wa’adin sa na shekaru takwas da kuma Karamin Ministan Harkokin Fetur, Timepre Sylva, wanda shi ma ya yi gwamnan jihar kafin Dickon. Amma yanzu Sylva ya koma APC.
Don haka za a iya cewa Douye Diri dan takarar PDP, da bazar Dickson zai yi rawa kenan, shi kuma David Lyon na APC da bazar Sylva zai yi ta sa rawar.
Sai dai kuma akwai sauran ‘yan takara har 43 daga jam’iyyu daban-daban. Amma kuma kowa ya san dukkan su idan an fara fafatawa a wannan safiyar, to duk ‘yan kallon tirja-tirjan gwada karfi za su koma tsakanin PDP da APC.
APC dai ba ta taba mulkin jihar Bayelsa ba. Jiha ce ta PDP tsawon shekaru 20 kenan, tun daga 1999.
Shin ko PDP za ta yi tsaye galala a wannan zaben ta bari APC ta sabule ma ta wando a tsakiyar kasuwa?
Kada a manta, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan na nan, da wahala ya yarda APC ta bi shi har gida ta yi masa bi-ta-da-kulli, wai dukan kabarin kishiya.
Discussion about this post